Cin amanar makusanta ga cin zarafin ƙananan yara

Manhaja logo

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Na samu halartar wani taron ƙaddamar da littafin da wata matashiyar marubuciya ta wallafa da harshen Turanci, mai suna Shackles of Abuse, wato Sarƙaƙiyar Cin Zarafi, labarin bautar da ’ya’ya mata cikin lalata. Ko da yake ba ina son yin sharhi kan littafin ba ne, sai dai labarin da jigon littafin ya taɓo ne ya tava zuciyata, kuma na ga ya dace mu yi nazari a kansa cikin wannan mako.

Labaran da ke cikin wannan littafin suna da tsoratarwa da firgitarwa ainun, musamman irin yadda marubuciyar ta riƙa kwatanta halin da ta samu kanta a ciki da wasu yaran mata irinta, sakamakon rashin imani da rashin tausayin da wasu ’yan uwa na jini suka riqa nunawa a rayuwarsu, da kuma tursasa musu shiga mummunar rayuwa.

Littafin ya dubi halin ƙunci da baƙin ciki ne da wasu yara mata kan shiga sakamakon irin yadda wasu makusantansu, da suka haɗa da uba, ƙanin uba, ko ƙanin uwa, wa, abokin wa, da makamantan su ke jefa rayuwar su cikin wani hali na cin zarafi ko dai ta hanyar fyaɗe ko yin lalata da su ta hanyar tsoratarwa ko amfani da qarfi ko jan ra’ayinsu ta hanyar yaudara, da ke ɓata musu tarbiyya da rayuwa baki ɗaya.

Ba baƙon labari ba ne a ji cewa, wani uba ya yi wa ‘yar sa ciki, ya yi lalata da ita ko ya yi wa wata ƙaramar yarinya cikin ’ya’yansa ko na makwafta fyaɗe. Ko kuma a samu wani ɗan uwa na jini da aka amince masa a cikin gida yana lalata da wata daga cikin ’ya’ya mata na gidan ko ‘ya’yan ‘yar uwarsa ko ɗan uwansa. Wannan cin amana da cin mutuncin ɗan Adam da ake yi wa ’yan mata da ƙananan yara cikin yanayin da ake ganin akwai yarda da aminci, babban abin damuwa ne, ba kawai ga yaran da ake yi wa wannan cin zarafi ba har ma da iyayen yaran, musamman mata.

Ana sanya firgici, tsoro da rashin yarda a zukatan yaran da suke girma da tunanin duk wani namiji ko makusancinsu ba abin yarda ba ne, mugu ne ko azzalumi ne da ke shirin cutar da su da lalata makomarsu.

Akasari masu aikata irin wannan mummunar halayya ba a cika hukunta su ko gurfanar da su gaban hukuma ba, saboda ana ganin matsala ce ta cikin gida bai kamata a tona asirin abin da ya faru ba, don kada a vata sunan yarinya ko wanda ya aikata mata wannan mummunar aika-aika. Don haka ba sa sanin illar abin da suka aikata da haɗarin sa ga tunani ko ɗabi’unta da mu’amalarta da sauran maza na cikin gida da na waje.

Wani lokaci a kan samu kuskuren haɗin bakin uwa ko sakaci da kawar da kanta, idan ya yi yawa, ga mu’amalar da ke faruwa tsakanin uba da ‘yar sa, ko ƙanin uwa da ‘yar ta, da sauran irin wannan alaqa, ba tare da ta yi bincike ko tsawatarwa kan wasu abubuwan da ta gani yana faruwa a tsakanin su ba. Tana ganin kamar yarda ce, haɗuwar jini ne ko zumunci ne. Alhalin tana iya yiwuwa abin da shi wannan uba ko ɗan uwa yake yi wa wannan yarinya a cikin ɗaki ko a ɓoye ba abu ne mai kyau ba, kuma ya saɓa wa tarbiyya ta al’ada da addini.

Wasu yaran suna tsoron bayyana abin da ke faruwa a tsakanin su da makusantan su ne, saboda tunanin ba za a yarda da su ba, ko za a zarge su da yi musu sharri ko ɓata suna. Ko kuma idan waɗannan mazajen sun yi musu wata barazanar kisa ko yaudarar za su basu kuɗi ko wani abin duniya da yaran ke kwaɗayin samu. Don haka sai su yi gum da bakin su, abin na ta faruwa a ɓoye, har sai Allah ya tona asirin su. Kafin a farga da wuri tuni ɓarnar da ake gudu ta auku. An koyawa yarinya lalata da maza, ko an nuna mata wata rayuwar da bai kamata a shekarun da take ta sani ba.

A irin wannan yanayi, waɗanda ake bai wa ko ya kamata su riqe amanar tarbiyyarsu ne suke cin wannan amana, su ne suke sauya rayuwar yaransu da kansu. A ƙarshe a ga yarinya tana yin wani abu da ya saɓawa hankali da tarbiyya har a shiga ɗora wa wasu da sunan maƙiya ko aljannu, domin yadda abin ya fara tava mata ƙwaƙwalwa ko ya jirkita mu’amalarta ta da ta sauran jama’a.

Babu wata ƙididdiga a hukumance da ake da ita na adadin yawan yaran da ake lalatawa rayuwa ko waɗanda ake yaudara a jefa rayuwar su cikin ƙuncin rashin kyakkyawar makoma, da zubewar darajar kai. Saboda yadda yaran da iyayensu ke kunyar bayyana abin da ya faru da kuma ɓoyewa saboda gudun ɓata sunan wanda ya aikata ɓarnar. Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta yi hasashen a cikin yara 10 shida daga cikin su an taɓa yi musu fyaɗe ko wani nau’i na cin zarafi yayin da suke gaban iyayensu ko hannun wasu makusantan su.

Ana samun cin zarafi ko cin amanar tarbiyya da raino a kowacce irin al’umma, ƙabila ko addini. A tsakanin ’yan ƙauye gidadawa ko wayayyu ’yan boko. A ƙasashen Turawa, Larabawa, ko baƙaƙenmu na Afirka. Sai dai an gano cewa fiye da kashi 95 cikin ɗari na irin waɗannan munanan halaye za a iya kaucewa faruwar su da magance su ba tare da sun yi illa ba, amma sakaci da rashin kula ko nuna damuwa shi yake ƙara munana abin.

Fiye da kashi 50 cikin ɗari na cin zarafin da ake yi wa ƙananan yara daga makusantan su ne waɗanda su ma suke da nauyin tarbiyyar yaran a kansu. Yayin da ake cewa kimanin kashi 25 cikin ɗari na yara masu alamun shiga shekarun balaga daga 12 zuwa 17 da ake samun rahoton an ci zarafin su na kusa da su ne yake fara sa su cikin wannan rayuwar.

Ba ’ya’ya mata kaɗai ake yi wa cin zarafi ba, har da maza. Sai dai ƙididdiga na nuna cewa, an fi cin zarafin yara mata fiye da maza, duk kuwa da kasancewar ba a cika kai hankali ko sa ido a kan nasu ɓangaren ba. Suleiman wani yaro ne mai kimanin shekaru 12, wanda wata bazawara ƙanwar mahaifinsa ta riƙa koyawa lalata tana kwanciya da shi ba tare da sanin kowa ba, har kuma hakan ya yi tasiri a rayuwar sa wajen mu’amalarsa da sauran mata da ya riƙa hulɗa da su bayan ya girma.

Yara maza da mata da aka buɗe musu ido da jima’i ko hanyoyin saduwa tsakanin mace da namiji, ko tsakanin jinsi guda, suna fuskantar wata matsala ta ƙwaƙwalwa inda suke girma cikin wata ƙazamar rayuwa da kullum suke nadama da takaicinta. Za su riƙa aikata wasu abubuwa na fasiƙanci, ko bin maza, ko mata barkatai ba tare da suna samun wani jin daɗi daga abin da suke aikatawa ba. Wanda hakan ke cutar da lafiyar tunaninsu, da zamantakewar su da mutane.

A makon da ya gabata, Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani tsari na kakkave ɓatagari da ke aikata munanan laifuka da ayyukan rashin tarbiyya a dukkan faɗin jihar, inda daga ciki ya haɗa da rufe gidajen rawar Gala da gidajen karuwai, saboda kasancewarsu mafakar ɓarayi da ’yan fashi. Abin takaici daga cikin matan da aka kama har da ƙananan yara da ba su wuce shekaru goma sha biyu zuwa sha biyar ba. Wasu ma an same su da ciki, wasu da ƙananan goyo. Duk kuma waɗannan abubuwan na da nasaba da muhallin da yaran suka tashi da abubuwan da wasu maciya amana da makusanta suka koya musu ne.

Lallai ne iyaye su zama masu kula da sa’ido kan irin shaƙuwa da yaransu kan yi da wasu manya makusanta, ko waɗanda ba su aminta da halayensu ba. Sannan su kula da irin ’yan’uwan da waɗannan yara ke tsoron zuwa kusa da su, saboda mai yiwuwa akwai abin da suke yi musu marar kyau da yaran basa jin daɗinsa. Ko wata barazana da suke yi musu, don su tsorata yaran su amince musu. Ita ma kuma gwamnati ta fahimci cewa, sanya irin waɗannan yara a cibiyoyin gyaran tarbiyya zai taimaka musu wajen canja halayensu da harkokin su na rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *