Cin amanar makusanta ga cin zarafin ’ya’ya mata

Daga ABBA YAKUBU ABDULLAHI

A ƙarshen makon da ya gabata na samu halartar wani taron ƙaddamar da littafin da wata matashiyar marubuciya Aisha Hamza Kallari ta wallafa da harshen Turanci, mai suna ‘Shackles of Abuse’, wato Sarƙaƙiyar Cin Zarafi, labarin bautar da ’ya’ya mata cikin lalata. Kodayake ba ina son yin sharhi kan littafin ba ne, sai dai labarin da jigon littafin ya taɓo ne ya taɓa zuciyata, kuma na ga ya dace mu yi nazari a kansa cikin wannan mako.

Labaran da ke cikin wannan littafin suna da tsoratarwa da firgitarwa ainun, musamman irin yadda marubuciyar ta riƙa kwatanta halin da ta samu kanta a ciki da wasu yaran mata irinta, saboda rashin imani da rashin tausayin wasu ’yan uwa na jini da suka riƙa uzzurawa rayuwarsu, da tursasa musu shiga mummunar rayuwa.

Littafin ya dubi halin ƙunci da baƙin ciki ne da wasu yara mata kan shiga sakamakon irin yadda wasu makusantan su, da suka haɗa da uba, ƙanin uba, ko ƙanin uwa, wa, abokin wa, da makamantan su ke jefa rayuwarsu cikin wani hali na cin zarafi ko dai ta hanyar fyaɗe ko yin lalata da su ta hanyar tsoratarwa ko amfani da ƙarfi ko jan ra’ayinsu ta hanyar yaudara, da ke vata musu tarbiyya da rayuwa baki ɗaya.

Ba baƙon labari ba ne a ji cewa, wani uba ya yi wa ’yarsa ciki, ya yi lalata da ita ko ya yi wa wata ƙaramar yarinya cikin ’ya’yansa ko na makwafta fyaɗe. Ko kuma a samu wani ɗan uwa na jini da aka amince masa a cikin gida yana lalata da wata daga cikin ’ya’ya mata na gidan ko ’ya’yan ’yar uwarsa ko ɗan uwansa. Wannan cin amana da cin mutuncin ɗan Adam da ake yi wa ’yan mata da ƙananan yara cikin yanayin da ake ganin akwai yarda da aminci, babban abin damuwa ne, ba kawai ga yaran da ake yi wa wannan cin zarafi ba har ma da iyayen yaran, musamman mata.

Ana sanya firgici, tsoro da rashin yarda a zukatan yaran da suke girma da tunanin duk wani namiji ko makusancinsu ba abin yarda ba ne, mugu ne ko azzalumi ne da ke shirin cutar da su da lalata makomarsu.

Akasari masu aikata irin wannan mummunar halayya ba a cika hukunta su ko gurfanar da su gaban hukuma ba, saboda ana ganin matsala ce ta cikin gida bai kamata a tona asirin abin da ya faru ba, don kada a ɓata sunan yarinya ko wanda ya aikata mata wannan mummunar aika aika. Don haka ba sa sanin illar abin da suka aikata da haɗarin sa ga tunani ko ɗabi’unta da mu’amalarta da sauran maza na cikin gida da na waje.

Wani lokaci a kan samu kuskuren haɗin bakin uwa ko sakaci da kawar da kanta, idan ya yi yawa, ga mu’amalar da ke faruwa tsakanin uba da ’yarsa, ko qanin uwa da ’yar ta, da sauran irin wannan alaƙa, ba tare da ta yi bincike ko tsawatarwa kan wasu abubuwan da ta gani yana faruwa a tsakanin su ba. Tana ganin kamar yarda ce, haɗuwar jini ne ko zumunci ne. Alhalin tana iya yiwuwa abin da shi wannan uba ko ɗan uwa ya ke yi wa wannan yarinya a cikin ɗaki ko a ɓoye ba abu ne mai kyau ba, kuma ya saɓa wa tarbiyya ta al’ada da addini.

Wasu yaran suna tsoron bayyana abin da ke faruwa a tsakanin su da makusantan su ne, saboda tunanin ba za a yarda da su ba, ko za a zarge su da yi musu sharri ko ɓata suna. Ko kuma idan waɗannan mazajen sun yi musu wata barazanar kisa ko yaudarar za su ba su kuɗi ko wani abin duniya da yaran ke kwaɗayin samu. Don haka sai su yi gum da bakin su, abin na ta faruwa a ɓoye, har sai Allah ya tona asirinsu. Kafin a farga da wuri tuni ɓarnar da ake gudu ta afku. An koyawa yarinya lalata da maza, ko an nuna mata wata rayuwar da bai kamata a shekarun da take ta sani ba.

A irin wannan yanayi, waɗanda ake bai wa ko ya kamata su riƙe amanar tarbiyya su ne suke cin wannan amana, su ne suke sauya rayuwar yaransu da kansu. A ƙarshe a ga yarinya tana yin wani abu da ya savawa hankali da tarbiyya har a shiga ɗora wa wasu da sunan maƙiya ko aljannu, domin yadda abin ya fara tava mata ƙwaƙwalwa ko ya jirkita mu’amalarta ta da ta sauran jama’a.

Babu wata qididdiga a hukumance da ake da ita na adadin yawan yaran da ake lalatawa rayuwa ko waɗanda ake yaudara a jefa rayuwar su cikin ƙuncin rashin kyakkyawar makoma, da zubewar darajar kai. Saboda yadda yaran da iyayensu ke kunyar bayyana abin da ya faru da kuma ɓoyewa saboda gudun vata sunan wanda ya aikata varnar. Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta yi hasashen a cikin yara 10 shida daga cikin su an taɓa yi musu fyaɗe ko wani nau’i na cin zarafi yayin da suke gaban iyayensu ko hannun wasu makusantansu.

Ana samun cin zarafi ko cin amanar tarbiyya da raino a kowacce irin al’umma, ƙabila ko addini. A tsakanin ’yan ƙauye gidadawa ko wayayyu ’yan boko. A ƙasashen Turawa, Larabawa, ko baƙaƙenmu na Afirka. Sai dai an gano cewa fiye da kashi 95 cikin ɗari na irin waɗannan munanan halaye za a iya kaucewa faruwarsu da magance su ba tare da sun yi illa ba, amma sakaci da rashin kula ko nuna damuwa shi ya ke ƙara munana abin.

Fiye da kashi 50 cikin ɗari na cin zarafin da ake yi wa ƙananan yara daga makusantan su ne waɗanda su ma suke da nauyin tarbiyyar yaran a kansu. Yayin da ake cewa kimanin kashi 25 cikin ɗari na yara masu alamun shiga shekarun balaga daga 12 zuwa 17 da ake samun rahoton an ci zarafin su na kusa da su ne ya ke fara sa su cikin wannan rayuwar.

Ba ’ya’ya mata kaɗai ake yi wa cin zarafi ba, har da maza. Sai dai ƙididdiga na nuna cewa, an fi cin zarafin yara mata fiye da maza, duk kuwa da kasancewar ba a cika kai hankali ko sa ido a kan nasu ɓangaren ba. Suleiman wani yaro ne mai kimanin shekaru 12, wanda wata bazawara ƙanwar mahaifin sa ta riƙa koyawa lalata tana kwanciya da shi ba tare da sanin kowa ba, har kuma hakan ya yi tasiri a rayuwarsa wajen mu’amalarsa da sauran mata da ya riqa hulɗa da su bayan ya girma.

Wannan labarin ya so ya yi kama da na Mariya mai shekaru goma sha uku da babanta ya riqa yaudarar ta yana sa mata maganin barci cikin nama, yana amfani da ita cikin dare tana cikin barci ba tare da mahaifiyar ta ko wani ya lura ba, har sai da ciki ya ɓulla. Ko kuma sa’arta Zuwaira da wani ƙanin babanta ya yaudara da sunan yana son ta daga nan ya fara mata wasannin banza, tun tana nuna qin amincewa da jin kunya har dai ta fara jin daɗin abin. Daga bisani ya samu nasarar yaudarar ta har ya fara amfani da ita, bayan ya lalata mata budurci. Lokacin da ta ji ta kamu da son sa, shi kuma sai ya guje ta, sai dai duk lokacin da sha’awarsa ta motsa ya je gidan su ko ya kira ta wani waje ya biya buƙatarsa. A dalilin haka halayyar wannan yarinya ta canza ta shiga wani ƙunci da damuwa mai tsanani.

Ita ma Grace misalin haka ne ya faru da ita, yayin da wani mai gadin gidansu da ya ke kula da su, bayan iyayen sun fita aiki, ya fara koya mata lalata, ta hanyar yi mata wasannin banza da taɓa mata wasu sassan jikinta da bai dace yana kai hannun sa ba. Da haka har yarinyar ta fara sabawa da shi, wani lokacin kuma ta bi malaman makarantar su ko abokan karatun ta na makaranta. Duka waɗannan abubuwan na faruwa ne a kan idon wasu iyayen ba tare da sun lura ko sun sa hankali sun fahimci mai ya ke faruwa ba.

Ƙalubale ne babba a kan iyaye da masu kula da raino da tarbiyyar yara, su riƙa kula da mu’amalar su da ’yan uwansu na gida da yayyensu ko masu kula da hidimomin su na gida. Abubuwa da dama na faruwa a irin wannan alaqa ta makusanta da zumuntar abokan zama na gida ɗaya ko maƙwaftaka, da wajen karatu. Wannan lalata tana faruwa a ɓoye ba tare da an ankara da wuri ba.

Hatta wasu abubuwa da suke faruwa na shaye-shaye ko ɗauke ɗauke da ƙananan shekaru, musamman ga yara maza suna fara wa ne daga gida ta dalilin wani gurɓataccen makusanci, ɗan uwa ko maƙwafci. Haka a gefen rayuwar mata ana samun fara lalacewar yarinya akasari daga gida, ba lallai sai daga namiji ba, har daga yayye mata waɗanda ke jan ƙannensu mata suna koya musu bin maza, ko harkar maɗigo da shaye-shaye, a cikin gida ba tare da an lura da wani abu makamancin haka na faruwa ba.

Sanya ido, kula da hattara wajen tarbiyyar yara abu ne mai muhimmanci sosai, domin shi mai tarbiyya tamkar makiyayi ne ko mai noman rani kullum a cikin ban ruwa ya ke, ana nasiha ana tsawatarwa, ana rakawa da addu’a. Sai dai kuskure ne yawan zargi, rashin yarda da tsangwama. Hakan na saurin lalata dangantaka, ɓata zumunci da rashin samun sakewa da juna a mu’amala ta zumunci da harkokin yau da gobe.

Sannan iyaye su daina ɓoye al’amarin cin zarafi irin na fyaɗe ko cin amana ta hanyar kai ƙorafi ga hukumomi domin ɗaukar matakin da ya kamata bisa doka, saboda hana cigaba da faruwar al’amarin, da nuna darasi ga wasu masu niyyar yin irin haka. Raba yara mu’amala da manya waɗanda suka fi su wayewa da yawan shekaru, don kaucewa koyon wasu halayen da ba su kamata ba, ko aikata musu wani abu da zai iya cutar da rayuwarsu.

A duk lokacin da aka lura yaro ko yarinya na ƙorafi ko nuna rashin sakewa kusa da wani babba ko da kuwa jininsu ɗaya to, a yi gaggawar yin bincike da sauraron uzurin sa ko kukan ta, kada a riƙa gwaɓeta ko kyararta don ana ganin ƙorafin da ta ke yi bai kamata a ce ya faru ba. Ko kuma a riƙa ganin ai kamar wane ko wance ba za su aikata haka ba.

Allah ya sa mu fi ƙarfin zukatanmu. Ya kare mu da zuri’armu daga faɗawa mugun hannu, da lalacewar tarbiyya. Amin.