Cin gashin kai: Abinda ya sa har yanzu ƙananan hukumomi ba su fara karɓar kuɗi kai-tsaye ba

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƙananan hukumomin Nijeriya (ALGON), ta ce akwai buƙatar baki ɗaya ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar su buɗe asusu a Babban Bankin ƙasar (CBN) domin samun kuɗaɗensu kai-tsaye daga Gwamnatin Tarayya.

Shugaban ƙungiyar, Bello Lawal Ƴanɗaki ya bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ya ce hakan yana da muhimmanci ga aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli na ba su ƴancin cin gashin kansu daga gwamnatocin jihohi.

Haka kuma Ofishin Sirri na kula da Kuɗaɗe na Ƙasa (NFIU) zai sanya ido ga ciyamomi wajen ganin sun sarrafa kuɗaɗen bisa gaskiya da adalci da kuma a tsarin shugabanci na gari.

Wata majiya ta ce tuni Gwamnatin Tarayya ta fitar da wani kwamitin yaƙi da rashawa da aka samar ƙarƙashin hukumomin ICPC da EFCC don binciken ciyamomi da wasu jami’ai da ke da hannu a lamuran da suka shafi rashawa.

Shugaban ne ALGON, wanda ya gana da manema labarai a Katsina, Babban Birnin jihar Katsina, ya koka kan yadda aka samu jinkiri wajen fara bai wa ƙananan hukumomin kuɗaɗen nasu.

Ya kuma ce hakan ya samu ne sakamakon rashin bada asusun banki ga Kwamitin Asusun Tarayya da Raba kuɗaɗe (FAAC) wanda shi zai jagoranci biyan kuɗaɗen.

Ya ƙara da cewa, suna cigaba da gudanar da shirye-shirye don tabbatar da cimma hakan wanda a yanzu CBN ya na jiran umarni daga Gwamnatin Tarayya don fara buɗe asusun.

Bugu da ƙari, wata majiya daga zaman FAAC ta ce ana shirin fitar da tsare-tsaren raba kuɗaɗen waɗanda suka kai Naira biliyan 361.754 da Gwamnatin Tarayya ta ware wa ƙananan hukumomin.