Cin gashin kan ƙananan hukumomi: Nasihar Tinubu ga gwamnoni

Kalaman da shugaba Bola Tinubu ya yi a baya-bayan nan game da ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi ya haifar da zazzafar muhawara game da tsarin mulkin Nijeriya da yadda ƙananan hukumomi ke ci gaba da yin biyayya ga gwamnoni. Shugaban ya yi magana kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana takun saa da gwamnonin jihohi kan ’yancin ƙananan hukumomi.

Shugaba Tinubu ya musanta raɗe-raɗin rashin jituwa tsakaninsa da gwamnonin kan yunƙurinsa na samar da ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar nan, ya ƙara jaddada ƙudurin da ya yi tun da farko kan tanadin tsarin mulkin ƙananan hukumomi.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi ga gwamnonin jihohin da suka kai masa ziyarar sabuwar shekara, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

Da yake bayyana ƙudirinsa kan ƙananan hukumomi da cin gashin kansu, shugaban ƙasan ya jaddada muhimmancin hakan ga ci gaban ƙasa tare da kawar da jita-jitar rashin jituwa da gwamnoni.

Ya ce, “Ba za mu yi faɗa a tsakaninmu ba. Zan jagoranci canji. Ku yi iko a ƙananan hukumominku. Kuna iya maido da fatan jama’a ta hanyar samar da abin da mutane suke tsammani a matakin farko. Akwai jita-jita cewa mun samu saɓani kan cin gashin kan ƙananan hukumomi. A’a kawai a kawo cigaba a ƙananan hukumomi.”

“Babu wanda yake so ya ƙwace su daga gare ku, amma muna buƙatar haɗin gwiwa. Mu yi aiki tare kuma mu tabbatar da cewa Nijeriya ta amfana da hakan,” inji Shugaba Tinubu, yana tabbatar wa gwamnonin.

Muna ganin shugaban ƙasa ya yi abin da ya dace ta hanyar kwantar da hankulan gwamnoni tare da kawar da fargabarsu kan sauye-sauyen da ake yi a ƙananan hukumomi. Gwamnonin Jihohin 36 ba su da wani abin tsoro domin gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin aiwatar da tsarin mulki ne kawai da kuma hukuncin da Koli ya yanke game da cin gashin kan ƙananan hukumomi. Kundin tsarin mulkin Nijeriya a fili ya kafa ƙananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnati, tare da tanade-tanade na cin gashin kansu na mulki da na kuɗi. Sai dai a tarihi, gwamnonin jihohi sun ci gaba da riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi ta hanyar tsarin asusun ajiyar ƙananan hukumomi na jiha (SJLGA). Wannan tsari dai ya mayar da ƙananan hukumomi baya wajen gudanar da mulki. Don haka, akwai buƙatar sake fasalin tsarin.

Tabbacin da kuma goyon bayan da shugaba Tinubu ya bayar ga gwamnonin jihohi, waɗanda ke riƙe da muhimman muƙaman siyasa da tsarin tattara ƙuri’u, zai taimaka matuƙa wajen samar da shugabanci a matakin ƙananan hukumomi. Wannan tsari na aiki da dabaru yana nuna irin tasirin Shugaba Tinubu da hazaƙarsa wajen samar da ci gaban ƙananan hukumomi, shugabanci nagari, da kuma tsarin jagoranci na kowa da kowa.

Muhimmancin wannan dabarar siyasa da ake ganin tana da yawa. Abin da ya fi dacewa a nan take shi ne kawar da shubuhohi da takun saka tsakanin gwamnatocin Jihohi da na tarayya kan matakin da ya kamata ya ɗauka a kan ƙananan hukumomi. Wannan zai iya daƙile ci gaban zamantakewa, tattalin arziki da siyasa a matakin farko. Hakan ya sanya gwamnonin su yada tsarin ake yi a yanzu, inda gwamnoni ke zaɓar shugabannin ƙananan hukumomi ta hanyar zaɓukan da ba su da tabbas ko kwamitocin riƙon kwarya, wanda ke gurgunta tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida.

Wataƙila abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda shugaban ƙasa ya jajirce a kan gwamnonin kan daƙile yadda tsarin ke cusa cin hanci da rashawa da rashin gaskiya a harkokin ƙananan hukumomi. Gwamnonin sun fahimci cewa, idan ba tare da kula da kuɗaɗensu kai tsaye ba, ƙananan hukumomi ba za su iya ɗaukar nauyin al’ummar mazaɓarsu ba, ta yadda za a samar da kyakkyawan yanayi da magance almundahana da rashawa.

Rikicin da ke faruwa tsakanin ƙananan hukumomi a jihar Edo da Gwamna Monday Okpebolo ya yi daidai da irin ƙalubalen da ke gaban ƙananan hukumomi na cin gashin kansu. Shisshigin da Ministan Kuɗi, Wale Edun ya yi, na goyon bayan ƙananan hukumomi (waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin PDP) ya nuna yadda gwamnatin tarayya ta yi bara’a da wannan matsala, wanda ya yi daidai da nasihar da shugaban ƙasa ya yi wa gwamnoni.

Hujjar samun ‘yancin cin gashin kan aananan hukumomi ya wuce la’akarin doka da siyasa. ƙananan hukumomi, idan aka ba su kuɗi da kuma sarrafa su yadda ya kamata, suna aiki ne a matsayin ginshiƙai na ci gaban ƙasa. Kusancinsu da al’ummomin gida yana ba su damar ganowa da magance takamaiman buƙatun al’umma.

Tsarin da ake yi yanzu yana haifar da giɓin dimokuraɗiyya a matakin ƙananan hukumomi. Lokacin da gwamnoni ke zaɓar shugabannin ƙananan hukumomi, hakan ya saɓa wa aa’idar wakilcin dimokraɗiyya da riƙon amana. Samun cin gashin kan ƙananan hukumomi na gaskiya zai ba da damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na gaskiya da kuma samar da gasa ta siyasa a matakin farko. Hakan zai ƙarfafa gwiwar al’umma wajen gudanar da mulki tare da samar da maslaha kai tsaye tsakanin shugabannin ƙananan hukumomi da waɗanda suka zaɓe su. Wannan dangantakar kai tsaye tsakanin shugabanni da shugabanni tana da muhimmanci ga ci gaban dimokuraɗiyya.

Domin Nijeriya ta samu ci gaba mai ma’ana da dunƙulewar dimokuraɗiyya, akwai muhimman canje-canje. Dole ne fadar shugaban ƙasa ta nuna aniyar siyasa don aiwatar da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasar kan cin gashin kan ƙƙnanan hukumomi. Wannan yana buƙatar tsayawa tsayin daka na gwamnoni da aiwatar da hanyoyin ba da tallafi kai tsaye ga ƙananan hukumomi.

Yakamata Majalisar Dokoki ta ƙasa ta ƙarfafa tsarin dokoki na kare cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Tsarin tarayya na gaskiya da mulkin dimokuraziyya ba za su wanzu ba sai da ƙananan hukumomi masu cin gashin kansu. Halin da ake ciki a halin yanzu, inda gwamnonin jihohi ke aiki a matsayin masu mulkin ƙananan hukumomi, ya saɓa wa ƙa’ida da tsarin mulkin Nijeriya. Har sai an magance wannan muhimmin al’amari, alƙawarin ci gaba na gaskiya da kuma dimokraɗiyya za su wanzu.