Cinikayyar ƙananan kayayyakin amfanin yau da kullum na tafiya yadda ya kamata a Sin

Daga CMG HAUSA

Wani rahoton hadin gwiwa na kamfanonin Bain & Company, da Kantar Worldpanel, masu bibiyar harkokin da suka shafi cinikayya, ya nuna cewa, cinikayyar kananan kayayyakin amfanin al’umma na yau da kullum na gudana cikin yanayin karko a kasar Sin, duk da kalubalen da ake fuskanta na bazuwar annobar COVID-19.

Rahoton ya ce sashen cinikayyar kananan kayayyakin amfanin al’umma na yau da kullum na kasar Sin ko FMCG a takaice, ya jurewa matsaloli masu alaka da samar da kayayyaki, da koma bayan tattalin arziki, saboda matsin da annobar COVID-19 ta haifar.

Kaza lika rahoton ya ce sashen na FMCG, ya bunkasa da kaso 3.6 bisa dari a shekara guda, tsakanin rubu’o’i 3 na farkon shekarar 2022.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa