Cinikayyar waje ta hajojin Sin ta bunƙasa da kaso 10.4 bisa ɗari cikin watanni 7 ba bana

Daga CMG HAUSA

Cinikayyar waje ta hajojin ƙasar Sin ta bunkasa da kaso 10.4 bisa dari cikin watanni 7 na bana, inda darajar kuɗaɗen cinikayyar ya kai kudin Sin tiriliyan 23.6, wato kimanin dalar Amurka tiriliyan 3.5 ke nan.

Hukumar kwastam ta ƙasar, ta ce mizanin kayayyakin da ƙasar ke fitarwa ya karu da kaso 14.7 bisa ɗari a shekara, zuwa yuan tiriliyan 13.37, yayin da na hajojin da ake shigowa da su ya ƙaru da kaso 5.3 bisa ɗari a shekara, zuwa yuan tiriliyan 10.23.

Alƙaluman hukumar ta kwastam sun nuna cewa, cinikayyar Sin da gamayyar ƙasashen yankin kudu maso gabashin Asiya, ta ƙaru da kaso 13.2, kana ta Sin da tarayyar turai ta ƙaru da kaso 8.9 bisa ɗari, yayin da ta Sin da Amurka ta karu da kaso 11.8 bisa ɗari cikin shekara guda.

A ɗaya hannun kuma, tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, cinikayyar Sin da ƙasashen dake cikin shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya ta ƙaru da kaso 19.8 bisa dari, yayin da ta Sin da ƙasashen dake cikin gamayyar haɗin gwiwar raya tattalin arziki ta RCEP, ta ƙaru da kaso 7.5 bisa ɗari a shekara.

Da yake tsokaci game da hakan, kakakin hukumar kwastam ta ƙasar Sin Li Kuiwen, ya ce a watan Yuli, cinikayyar Sin da ƙasashen dake cikin gamayyar haɗin gwiwar raya tattalin arziki ta RCEP, ta kai darajar yuan tiriliyan 1.17, wato ƙaruwar kaso 18.8 bisa ɗari a shekara guda, wanda kuma hakan ya bunƙasa ɗaukacin sassan cinikayyar waje da Sin ke gudanarwa, da kaso 5.6 bisa dari.

Fassarawar Saminu Alhassan