Cire tallafin fetur: Gwamnatin Tarayya ta ajiye sama da Naira tiriliyan ɗaya a cikin wata biyu – Tinubu

• Ya ce za a raba motocin sufuri 3000 a jihohi
• Ya ce sauran abubuwan jin daɗi na zuwa nan ba da jimawa ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a ranar Litinin cewa a cikin ƙasa da watanni biyu Gwamnatin Tarayya ta ajiye sama da Naira tiriliyan ɗaya sakamakon cire tallafin man fetur.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani jawabi da aka watsa wa ‘yan Nijeriya kan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a fannin tattalin arziki.

“A cikin ƙasa da watanni biyu, mun ajiye sama da Naira tiriliyan ɗaya da za a yi varnatarwa a kan tallafin man fetur da ba a samar da shi ba wanda kawai masu fasa-ƙwauri da wasu ‘yan damfara suke amfana. Yanzu za a yi amfani da wannan kuɗin kai tsaye kuma zai amfanar da ku da iyalanku,” inji shi.

Ya ce za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen da aka tara don tallafa wa masu ƙananan sana’o’i, ƙanana da matsakaitan masana’antu da kuma sayen motocin bas masu amfani da man CNG masu kujeru 20 guda 3,000 da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 100 da za a raba wa masu sufuri a faɗin ƙasar nan da dai sauransu.

“Wani ɓangare na shirin mu shi ne fitar da motocin bas a faɗin jihohi da ƙananan hukumomi don jigilar jama’a a farashi mai sauƙi.

Mun yi tanadin saka hannun jarin Naira biliyan 100 daga yanzu zuwa Maris 2024 don samun motoci 3000 masu kujeru 20 da ke amfani da man CNG.

“Waɗannan motocin bas ɗin za a raba su ga manyan kamfanonin sufuri a jihohin, ta hanyar amfani da ƙarfin tafiye-tafiye kowane gari. Kamfanonin sufuri masu shiga za su sami damar samun kuɗi a ƙarƙashin wannan wurin a kashi 9 a kowace shekara tare da lokacin biya na watanni 60.

“Hakazalika, muna kuma aiki tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙwadago domin ɓullo da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa. Ina so in gaya wa ma’aikatanmu wannan: bitar albashinku yana zuwa.

“Da zarar mun amince da sabon mafi ƙarancin albashi da kuma sake dubawa na gaba ɗaya, za mu yi tanadin kasafin kuɗin don aiwatarwa cikin gaggawa.

“Ina so in yi amfani da wannan damar don jinjina wa ma’aikata masu zaman kansu da yawa a cikin ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda tuni suka aiwatar da bitar albashi na gabaɗaya ga ma’aikata.

“Abin baƙin ciki, an samu raguwar da ba za a iya gujewa ba tsakanin cire tallafin da waɗannan tsare-tsaren suna zuwa gabaɗaya akan layi.

Ko yaya, muna hanzarta rufe tazarar lokaci. Ina roƙon ku don Allah ku kasance da bangaskiya ga iyawarmu don ceto da kuma damuwarmu don jin daɗin ku.

“Za mu fita daga wannan ƙangi. Kuma, saboda irin matakan da muka ɗauka, Nijeriya za ta samu nagartattun kayan aiki da kuma samun damar cin gajiyar makomar da ke jiran ta,” inji shi.

Shugaban ya ce dole ne Gwamnatin Tarayya ta cire tallafin man fetur saboda ba ta cika manufar da aka kafa ta ba.

“Gwamnatin da ta gabata ta ga irin wannan hatsarin da ke kunno kai. Tabbas, bai yi wani tanadi ba a cikin 2023 ƙaddamar da cire tallafi bayan Yuni na wannan shekara. Cire wannan tallafi ya zama babu makawa.

“Na yi alƙawarin gyara tattalin arziki don samun ci gaba mai ɗorewa ta hanyar yaƙi da manyan matsalolin da suka addabi tattalin arzikinmu.

“Tattalin arzikinmu yana cikin tsaka mai wuya kuma hakan yana cutar da ku. Farashin man fetur ya tashi. Abinci da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum su ma sun tashi. Iyali da kasuwanci suna fama. Abubuwa suna kama da damuwa da rashin tabbas.

“Na fahimci wahalar da kuke fuskanta. Ina fata akwai wasu hanyoyi. Amma babu. Da da akwai da na bi wannan hanya kamar yadda na zo nan don in taimaka kada in cutar da mutane da al’ummar da nake so,” inji shi.

Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta cika alƙawarin da ta ɗauka na samar da ilimi mai araha ga kowa da kowa da kuma bayar da lamuni ga ɗaliban manyan makarantu da ka iya buƙata.

“Babu wani ɗalibi ɗan Nijeriya da zai yi watsi da karatunsa saboda rashin kuɗi. Alƙawarinmu shi ne inganta rayuwar mutanenmu. A kan wannan ƙa’ida, ba za mu tava yin ƙasa a gwiwa ba,” inji shi.

Ya ce gwamnati za ta kuma sanya ido kan illolin da farashin canji da hauhawar farashin man fetur ke haifarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *