Cire tallafin mai: Ƙungiyar Ƙwadago za ta gudanar da zanga-zanga a faɗin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC, ta ce ta shirya tsaf domin tsunduma cikin gagarumar zanga-zanga a faɗin Nijeriya a ranar 1 ga watan Fabrairu, domin nuna rashin goyon bayan shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi na cire tallafin man fetur gaba ɗaya.

Ƙungiyar ta yanke shawarar ne a wani jawabin bayan taro da ta fitar a ranar Juma’a, wanda Shugaban ta na ƙasa, Kwamared Ayuba Wabba da kuma Babban Sakataren ta, Emmanuel Ugboaja su ka rattava wa hannu bayan taron majalisar zartarwar.

NLC ta ce kafin zanga-zangar ta ƙasa, rassan ta na jihohi za su fara yin gangami a baki ɗaya jihohi 36 da qasar nan a ranar 27 ga watan Janairu domin nuna rashin goyon baya ga cire tallafin man fetur.

Jawabin bayan taron ya nuna cewa cire tallafin man fetur zai jefa ma’aikata da ‘yan ƙasa cikin halin ni-‘ya-su sannan ya ƙara ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki da yake damun ƙasar.

“Saboda haka ne majalisar ƙoli ta yanke shawarar qin amincewa da ƙarin farashin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi domin ya nuna rashin tausayi ga wahalar da ‘yan ƙasa da ma’aikata su ka tsinci kansu a ciki a ƙasar nan.

“Rashin yarda da amincewa na ƙarin farashin man fetur ne ya sanya za mu shirya zanga a gaba ɗaya jihohi 36 na ƙasar nan a ranar 27 ga Janairu. “Da ga bisani kuma su mu rarraba wasiƙar gayyata ga dukka gwamnoni jihohi 36, inda da ga bisani kuma sai mu fito zanga-zangar ta ƙasa a ranar 1 ga watan Febrairu a Abuja,” in ji jawabin bayan taron.

Ƙungiyar ta kuma shawarci gwamnatin taraiya da ta gyara matatan man fetur ɗin ƙasar nan domin amfanin ‘yan ƙasa, maimakon cire tallafin man fetur da zai ƙara gallazawa talakawa.