Cire tallafin mai: Dalilin Buhari na bar wa magajinsa damar hukunci

*NNPC na buƙatar Naira tiriliyan uku a 2022

Daga MAHDI M. MUHAMMAD da SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ƙarshe dai Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ta yi watsi da cece-kucen da ake yi na buƙatar ko akasin haka wajen cire tallafin man fetur, inda ta ce, ta bar zaɓin aiwatar da hakan ga wanda zai gaji ofishin Shugaban Ƙasa a 2023, saboda yanayin halin da tattalin arzikin Nijeriya da ma na ’yan Nijeriya ke ciki a halin yanzu.

Kana kuma, idan shawarar ta wuce gaban Majalisar Dokoki ta ƙasa da ake sa ran za ta ba ta wasu ƙa’idoji ta hanyar yin kwaskwarima ga Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), to za a iya fitar da tallafin nan da Yuli 2023, bayan wata guda bayan sabuwar gwamnati dole ne a ƙaddamar da su.

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da wannan batu ne a ranar Talata yayin da ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa aka ɗage cire tallafin duk da cewa a baya ta ce za a cire shi a ƙarshen watan Yuni.

Shugaban ya ce, dole ne a samar da duk wasu tsare-tsaren da suka dace don daƙile illolin cirewar cikin watanni 18.

Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja bayan wata ganawa da shugaban.

Ya ce, tsare-tsaren, kamar yadda shugaban ya nuna, har yanzu ba a fara aiki ba, inda ya ƙara da cewa, da sa hannun Buhari, tallafin man fetur ba ya kan teburi a yanzu.

Ministan ya ce, gwamnati za ta ci gaba da jan hankalin shugabannin ƙungiyoyin qwadagon da tun da farko suka gabatar da wata zanga-zanga a faɗin ƙasar a ranar 27 ga watan Janairu domin nuna adawa da cire tallafin.

Ministan ya ce, majalisar zartarwar za ta ba da shawarar tsawaita wa’adin watanni 18 ga majalisar dokokin ƙasar domin aiwatar da dokar masana’antar man fetur (PIA) da za ta fara aiki a wannan watan Fabrairu.

“Ba mu da niyyar cire tallafin a yanzu. Shi ya sa muke yin wannan sanarwar. Muna kuma ganin tasirin shari’a. Akwai tanadin watanni shida a cikin PIA wanda zai ƙare a watan Fabrairu kuma shi ya sa muke fitowa muna cewa kafin ƙarewar wannan lokaci, kamar yadda na faɗa a baya, za mu shigar da majalisa. Mun yi imanin cewa wannan zai tafi ga majalisa; muna neman a gyara dokar ta yadda za mu kasance cikin doka,” inji shi.

Shugaban Buhari ya sanya hannu kan doka:
A ranar 16 ga watan Agusta, 2021 ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan ƙudurin dokar masana’antar man fetur.

Shugaba Buhari ya amince da ƙudurin dokar da majalisar dattawa da ta wakilai suka yi a farkon watan Yulin 2021.

Ana sa ran PIA za ta ƙara kwarin gwiwa ga masu zuba jari a Masana’antar Man Fetur ta Nijeriya da kuma samar da ƙarin damar yin aiki ga jama’a a cikin al’ummomin da ke karvar baƙuncin.

Ƙungiyar Ƙwadago ta dakatar da zanga-zanga a faxin ƙasar:
A halin da ake ciki, ƙungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) a ranar Talata ta dakatar da shirinta na gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar sakamakon shirin cire tallafin man fetur.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Shugaban NLC, Kwamared Ayuba Wabba ya ce, ƙungiyar za ta ci gaba da jan hankalin gwamnati kan muhimman batutuwan da suka shafi ’yan Nijeriya.

A wani labarin kuwa, Kamfanin Mai na Nijeriya, NNPC, ya nemi Naira tiriliyan uku don biyan kuɗin tallafin man fetur a shekarar 2022 bayan gwamnatin ƙasar ta fasa janye tallafin kamar yadda ta tsara a watan Yuni mai zuwa.

Ministar Kuɗi da Tsare-Tsare, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana hakan ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa.

Ta ƙara da cewa Nijeriya na buƙatar ta ƙara Baira tiriliyan biyu da rabi a cikin kasafin kuɗinta na 2022 don biyan kuɗin tallafin yayin da za ta gabatar da buƙatar gyaran ga ‘yan Majalisar Tarayya.

“A 2022, sakamakon ƙaruwar farashin mai a kasuwar duniya zuwa dala 80 kan kowace ganga ɗaya a yanzu, sannan kuma ƙiyasin NNPC ya nuna cewa ana shan litar mai miliyan 6.5 a kullum a Nijeriya, hakan zai sa mu samu ƙarin anaira tiriliyan uku a 2022,” inji ta.

A cewar ministar, Gwamnatin Tarayya na kashe kusan Naira biliyan 270 a kowane wata wajen biyan tallafin mai. Ta ƙara da cewa a yanzu an tanadi biliyan 443 ne kawai a kasafin kuɗi na 2022, wanda a da aka tsara za a biya daga Janairu zuwa watan Yuni kawai.

Majalisar ta duba buƙatar kamfanin mai na NNPC sannan ta umarci Ma’aikatar Kuɗi da Tsare-Tsare da ta fara tattaunawa da ‘yan majalisa don yi wa kasafin kuɗin kwaskwarima.

A gefe guda kuma, Majalisar Tarayya ta ƙaddamar da bincike kan yawan man da aka ce ‘yan Nijeriya na sha a kullum da kuma matatun mai na ƙasar biyo bayan fasa janye tallafin.

A 2021 gwamnatin Shugaba Buhari ta ce ta ware dala biliyan ɗaya don gyara matatar mai ta Fatakwal da ke Jihar Ribas.

Shi kuwa Shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya kuma Gwmanan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce tattalin arzikin Nijeriya “na tsaye cak”, yana mai cewa idan za a cire tallafin dole ne talakawa su amfana ba wasu ‘yan tsiraru ba.

Da yake magana da shugabannin ƙungiyar ƙwadago a Abuja ranar Laraba, Gwamna Fayemi ya ƙara da cewa ya zama dole ‘yan ƙwadago da gwamnoni su bi diddigin ƙiyasin da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Ya ƙara da cewa jihohi takwas ne kaɗai suke amfana da tallafin kai-tsaye, yana mai nuna damuwa kan cin hanci da rashawa da ya dabaibaye sashen mai da iskar gas a ƙasar.

“Gwamnoni ba za su yi shuru kan harkokin man fetur ba, dukkan ƙasashe maƙota da suka kewaye Nijeriya; Nijar da Ghana da Kamaru da Mali, na da farashin mai daidai da dala,” inji shi.

“Farashin mai a Nijeriya kuwa bai kai dala ba, amma muna ƙin cire tallafi har sai gwamnatin tarayya ta fuskanci matsalolin da take magana gaba-gaɗi.

A wani labarin mai kama da wannan, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, yana da isashshen man fetur don biyan buƙatun ‘yan Nijeriyar.

Garba Muhammad, mai magana da yawun NNPC ne ya bayar da wannan tabbacin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Muhammad ya shawarci jama’a da kada su riƙa sayen man fetur don gudun ƙarancin sa kuma su yi watsi da duk wata jita-jita da ke nuna akasin haka.

“La’akari da dokokin da ake da su a ƙasar, kamfanin NNPC ya himmatu matuƙa wajen tabbatar da tsaron makamashin ƙasar,” inji shugaban NNPC.