Cire tallafin mai: Gwamnan Taraba ya rage kuɗin makaranta da kashi 50

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ba da sanarwar rage kuɗin makaranta na jami’ar jihar da kashi 50% domin rage wa ‘yan jihar raɗaɗin tallafin man da aka cire.

Mai magana da yawun Gwamnan, Emmanuel Bello ne ya bayyana haka a Jami’ar Jihar Taraba, inda ya ce batun ilimi na daga fannonin da gwamnatin jihar ta bai wa fifiko.

Ya ce tuni Gwamna Kefas ya ayyana dokar ta ɓaci a fannin ilimin jihar domin bunƙasa shi.

Majiyarmu ta ce galibin ɗaliban jami’ar sun nuna jin daɗinsu da wannan mataki da Gwamnan ya ɗauka, inda suka ce hakan zai taimaka wa rayuwarsu.

Bello ya ce, “Wasu iyayen yara sun ce mawuyacin halin da cire tallafin mai ya je fa ya sa biya wa ‘ya’yansu kuɗin makaranta ya gagare su. Sun ce rage kuɗin makarantar zai ƙarfafa musu gwiwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *