Cire Tallafin Mai: Kotu ta daƙile aniyar NLC na shiga yajin aiki

Daga BSHIR ISAH

Kotun Ma’aikata mai zamanta a Abuja ta daƙile shirin Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) na shiga yajin aiki sakamakon cire tallafin mai.

Alƙali Olufunke Anuwe ne ya bai wa NLC da rassanta umarnin dakatar da ƙudirin shiga yajin aikin yayin zaman kotun a ranar Litinin.

NLC ta shirya fara yajin aikin ne ya zuwa ranar Laraba domin nuna rshin goyon bayanta kan matakin cire tallafin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *