
Daga ADAM MUHAMMAD a Gusau
Hukumar tsaro ta Civil Defense (NSCDC) reshen Jihar Zamfara, ta kama wani da ake zargi da busasshen ganyen tabar wiwi a ƙaramar hukumar Shinkafi.
An kama wanda ake zargin ne mai suna Kasimu Abubakar ɗan shekaru 40 a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, 2025.
Kwamandan rundunar ta jihar, Sani Mustapha a wani taron manema labarai a ranar Litinin ya ce kafin a kama shi, bayanan sirri daga jihar Legas sun yi nuni da cewa ana safarar tabar ne zuwa Zamfara, kuma hukumar inda suka tabbatar da kama buhun tabar a yayin da ake safararsa.
A cewarsa, a lokacin binciken farko, Kasimu Abubakar ya amsa laifinsa kuma ya tabbatar da sakamakon binciken da aka yi akansa.
Kwamanda Sani Mustapha ya cigaba da cewa, abubuwan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da, fakiti 70 da aka ɓoye acikin buhun da aka samu kan kuɗi 1,050,000.
Ya ce kowane fakitin ya kai N15,000 kuma ana sayar da shi akan kuɗi N25,000, wanda jimillar kuɗin ya kai N1,750,000, yayin da ya ce yana samun ribar Naira dubu ɗari bakwai.
Ya ƙara da cewa, wanda ake zargin yana kai wa gungun ƴan bindiga ne a ƙauyen Mashema da ke ƙaramar hukumar Zurmi.
“Wanda ake zargin ya bayar da cin hancin N1m ga ofishin shiyya ta Shinkafi domin a sake shi amma aka ki amincewa.”
“Binciken da aka gudanar ya gano wasu mutane biyu da ake zargin, wato Zayyanu da Ashiru. Hakazalika rundunarmu a jihar na kan sa ido kuma da zarar an kama su, za gabatar da su duniya ta sani”, inji shi.