Ciwo na na jiki ne ba na zuciya ba, ina ƙoƙarin rubutu don sha’awar da baiwar basu gushe ba – Saliha Abubakar Abdullahi Zaria

*Rubutu tamkar zazzaɓi ne, duk lokacin da masassarar sa ta taso, ɗaukar alƙalami da takarda ne kawai maganin ta, cewar Saliha

Daga AISHA ASAS

Waiwaye dai aka ce adon tafiya ne, yayin da rawar ‘yan mata kan ƙayatar ne a lokacin da su ke yin gaba suna dawowa baya. Idan aka yi zancen Adabin Hausa, dole ne a sanya marubuta mata da su ka fara rubutu tun lokacin da kai bai waye ba. Su ne marubutan da su ka fuskanci ƙalubale masu yawa kasancewar sun fara abin da Alummar Hausa ba su fara gani ba, don haka su ka jahilce shi har ta kai su na ma sa mumunar fahimta. Don haka labarin Adabin kasuwar Kano ba zai taɓa cika ba inhar ba a saka ire-iren waɗannan jajirtatun mata ba. Shafin Adabi na wannan sati shima ya waiwaya don gyara adon da ya ke yiwa masu karatu, ya ɗauko maku ɗaya daga cikin marubutan da suka yi shimfiɗar da yau matasan marubuta ke hutawa a kan ta. An dai ce yabon gwani ya zama dole, kuma dole ne a ce da mijin Iya Baba. Masu karatu idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Saliha Abubakar Abdullahi Zaria:

Mu fara da jin tarihin ki a taƙaice.
Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. Sunana Hajiya Saliha Abubakar Abdullahi Zaria. An haifeni a cikin garin Zaria (Zazzau) shekaru hamsin da su ka wuce, na yi makarantar Allo, Islamiyya da na ilmin Zamani (boko) duk a Zaria, na kammala karatun Makarantar Sakandire ɗina da na yi a ‘Government Girls Day Secondary School’ Ƙofar Gayan, a shekarar 1984. Ban samu goyon bayan ci gaba da karatu ba a lokacin, daga nan na yi aure a shekarar 1985. A halin yanzun ina tare da maigidana a garin Sakkwato, kuma Allah Ya albarkace mu da samun yara biyar, biyu mata, duk sun yi aure sun samu ƙaruwa, maza uku kowanne na neman ilmi gwargwado.

Zuwa yanzu ki na da littafai nawa?
Na rubuta littattafai goma sha biyar fitattu: ‘Wani Jinkiri, Zumuncin Zamani, Son Zuciya, Tun Ran Gini, Haihuwa Kyautar Allah, Rahima, Bege, Ba A Nan Take Ba, Sai Bango Ya Tsage, Ruwan Zuma, Yarda Da Ƙaddara, Edge of Faith, ‘Yar Baiwa, Halacci, Burina.

Ya za ki iya misalta yanayin darajar rubutu a lokacin da ki ka fara buga littafi?
A wancan lokacin marubutan sun san kansu, sun san darajar rubutun da ƙimarsa saboda har cikin ransu suke jin baiwar da Allah ya ba su, sun san muhimmancin saƙonnin da suke aikawa cikin rubuce-rubucensu da niyyar gyara cikin al’umma ta hanyar nishaɗi ba tare da tunanin samun kuɗi ko suna ba.

Ko akwai wani ci gaba ko ci baya da aka samu a yanzu wanda babu shi a baya a duniyar rubutu?
Ci gaban da aka samu yanzun su ne; ƙaruwar yawan marubuta maza da mata, ƙoƙarin kafa ƙungiyoyin marubuta cikin jihohinmu, samun kafafen sadarwa na zamani ma’ana yanar gizo-gizo wanda hakan ya bai wa yawancin marubuta damar baje kolin hikimarsu, da kuma samar wa marubuta damar shiga gasar gwada hikima da basirarsu har kuma a ba su wata kyauta don ƙara musu tallafi ko ƙwarin gwiwa kan abinda suke yi, to gaskiya waɗannan ci gaba ne sosai a duniyar rubutu na wannan lokacin.

Sai dai duk da haka an samu koma baya ta ɓangaren mutuwar kasuwar bugaggun littattafanmu a dalilin ha’incin ‘yan kasuwa, da kuma tahowar zamani, saboda yawanci makarantar ma sun fi son su ɗauki waya kawai su buɗe su karanta littafan da ake rubutawa ‘Online’ da su saya ainihin littafin da marubuci yai ƙoƙarin fitarwa.

Kin sanar da mu ki na zaune a Sakwatto. Ko akwai wata ƙungiya da ku ka kafa ta marubuta a jahar?
A da can mun yi ƙoƙarin inganta ƙungiyar ANA, reshen Jihar Sakkwato, ina iya tuna kaiwa da komowar da marubuci Malam Husaini Adamu Zuru ya yi, tare da Hajiya Hadiza Bunguɗu da ni kaina, da marigayi Alkanci, da wasu sauran tsirarun marubuta, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba, dole muka haƙura, daga lokacin kuma saboda wasu dalilai ban sake shiga cikin wata ƙungiyar ba, amma akwai ƙungiyar marubuta a Sakkwato a halin yanzun.

Ana cewa rubutun ku ya fi na marubutan zamanin nan. Shin me su ka rasa a nasu rubutun?
Abinda yawancin marubutan yanzun su ka rasa a nasu rubutun shi ne; inganci ta hanyar bin ƙa’idojin rubutun, dogon nazari, faɗaɗa bincike da neman shawarar manazarta don neman gyara da inganta labarinsu kafin su saki, ga kuma garaje, sai kiga cikin ƙanƙanin lokaci an wanzar da labari, kafin a yi haka ya karaɗe duniya, saɓanin irin namu da muka rinƙa rubutun a takarda, muna yi muna bincike, idan mun gama da ‘Manuscript’ sai mun ba malaman jami’a ko a ce manazarta sun duba sun yi mana gyara, sannan mu bayar a yi ‘typesetting’, a dawo mana da su mu yi ‘proofreading’ mu sake gyara kurakuren da aka nuna mana, so da yawa wajen sake bin labarin wajen gyare-gyaren kan ƙara buɗe mana ƙwaƙwalwa ki ga wani sabon ‘idea’ ya shigo mana, bayan mun gama mu sake maidawa a sake ‘typing kafin a kai ga maɗaba’a, can ma a yi aikin fitar da ‘plates, a taƙaice muna ɗaukan watanni daga lokacin rubutu zuwa lokacin da littafinmu zai fito kasuwa. Don ni ma a shekara guda littafi ɗaya nike fitarwa, saboda sai na tsaya bincike, nazari da neman shawarwari tukunna.

Ya ki ka ji a lokacin da ki ka fitar da littafin ki na farko?
Abinda na ji murna da farin ciki sosai kwatankwancin irin yadda mutum zai ji idan Ubangijinsa Ya biya masa wata buƙata da ya daɗe ya na roƙonsa, kwatsam sai ijabarsa ta sauka.

Wane lokaci ki ka fi sha’awar yin rubutu?
Gaskiya ban keɓe katamammen lokacin rubutu ba, zan iya ce miki na kan yi rubutuna ne duk lokacin da ‘idea’ ta taso ta na min yawo cikin kwanya, don haka na kwatanta miki rubutu tamkar zazzaɓi ne, duk lokacin da masassarar sa ta taso, ɗaukar Aalƙalami da takarda ne kawai maganinta.

Masu karatun mu za su so jin irin nasarorin da ki ka samu a harkar rubutu.

Ba za su lissafu ba, amma babban nasarata a harkar rubutu ita ce baiwar hikimar da basirar da Ubangijina Ya ba ni wanda har zan iya sarrafa kwanyanta in rubuta abinda jama’a za su karanta su fahimta, su ɗauki darasi ɗaya ko biyu su kuma amfana, dalilin haka suke min addu’oi duk rana ta Lillahi, ba ƙaramin abu ba ne a gareni. Nasara ta biyu ita ce yaba rubutuna da wasu daga cikin manyan jami’oinmu na Arewa suka yi har suka rinƙa turo min ɗalibansu suka yi bincike a kaina da ayyukana domin cika ƙa’idar samun digirinsu na farko a fannin Harshen Hausa. Watau Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, da Kuma ta Usman Ɗanfodiya da ke Birnin Sakkwato. Bayan wannan sai yai min arzikin jama’a, wanda kuwa Allah ya yi wa arzikin jama’a ya gama masa komai, duniya sai fatan gamawa lafiya.

Akwai ƙalubale?
Akwai ƙalubale kamar kusan kowacce rayuwar ɗan’adam. Bayan rashin samun goyon bayan da na fara samu kan rubutun bayan zuwana Sakkwato da gwagwarmayar da na sha, sun zama tarihi sai kuma ki rubuta littafan kina ji kina gani sai dai ki zuba ido kina kallo su yi ƙura saboda ba ki da zarafin bugawa, idan kuma har Allah ya taimake ki ya ƙaddare ki da samun hanyar buga littafin, sai a buga a kai kasuwa a sayar amma ‘yan kasuwan su tattara kuɗin su cinye ba tare da tausayi ko tsoron Allah a zukatansu ba, balle tunanin haƙƙin wani fa su ka ci, kuma in ba yafewa aka yi ba za su biya gobe ƙiyama, da yawa marubuta suna da wannan tabon, dalilin hakan kuma ya kawo naƙasa da durƙushewar da dama daga cikinmu.

Bayan waɗannan na fuskanci ƙalubalen rashin lafiya wacce ta tava ‘Spinal cord’ ɗina ya zama rubutun na yi min wuyan gaske, amma Alhamdu lillah tunda da sauran rayuwar, raunin na jiki ne ba na zuciya ba da taimakon Ubangiji ina ƙoƙarin rubutun don sha’awar da baiwar ma ba su gushe ba.

Subhanallah! Allah Ya kawo sauƙi, Ya sa kaffara ne.
Amin. Na gode.

Marubuta yanar gizo marubuta ne ko sai wanda ya buga littafi ne za a iya kira marubuci?
To a nan kai tsaye ba zan kirasu da sunan marubuta ba duk da yake cikinsu akwai masu ɗimbin hikima da basira tare da tsinkaya wajen rubutunsu fiye da rubutun wasu da su ka fitar da littafin ma, ga Kuma misali nan an gani wasu daga cikinsu na lashe gasar BBC, to da za su ƙara tsabtace rubutunsu a kuma buga labarinsu matsayin littafin da ko shekaru nawa zai yi za a iya ɗauka a karanta har ma a rinƙa nazarinsu, martabarsu za ta ɗaga sosai.

Shin kin kai matsayin da ki ke son kai a harkar rubutu ko da saura?
Kowanne ɗan’adam kan tsaya matsayin da Ubangijinsa ke son ganinsa a kai ne. Karɓuwar littafin marubuci cikin al’umma da nuna gamsuwarsu kan abinda yake rubutawa ba ƙaramin al’amari ba ne, ta wannan ɓangaren zan iya cewa Allah ya kai ni matsayin da nike so sai dai har gobe in dai da rayuwa akwai sauran gudunmuwa da zan ci gaba da bayarwa ta fannin rubutu tare da taimakon Ubangiji da samun ƙwarin gwiwar da masoya ke bani ta hanyar ɗimbin ƙauna da addu’oinsu.

Mene ne babban burin ki a harkar rubutu?
Babban burina na farko shi ne in samu waɗanda za su ɗauki littafin da na rubuta bayan na tashi daga jinya mai suna burina su maishe shi fim, ba don komi ba sai don faɗakarwar da ke cikin littafin, al’amari ne da ya shafi fannin lafiya, musamman cutar da ke samun yara wanda ruwa ke taruwa a ƙwaqƙwalwarsu, (Hydro cephalus), da sauran cututtukan da na yi bincike na yi rubutu a kansu, saboda fim ɗin ya fi saurin isar da saƙo lungu da saƙo musamman ga yawancin waɗanda irin waɗannan cututtukan ke addaba, ba kowanne ke da ilmin karanta littafi ba.

Burina na biyu shi ne; fatan ganin kasuwar marubuta littafai da ta mutu ta dawo hayyacinta, an ci gaba da harkar rubutu kamar da, ko ma fiye da da ɗin. Burina na uku; ina fatar Marubuta mu ci gaba da zaƙulo matsalolin da su ka addabi Arewacin ƙasarmu, musamman cin zarafin mata da yara ƙanana, sace-sacen mutane da Ta’addanci domin bada tamu gudumuwar wajen gyara ƙasarmu, kun dai san alƙalami ya fi Takobi. Ina fatan in ga al’umma ta gyaru ta fannin inganta tarbiyyar matasanmu don su ne tushen al’umma, sai uwa, uba mu kanmu iyaye mata mu gyara tarbiyyarmu ta inganta, mu kuma dage da adduo’i neman shiriyar ɗiyanmu, mu rinƙa tuna cewan mu ɗin ne makaranta ta farko wanda ‘ya’yan ke fara aza tubalin gina rayuwarsu. Allah ya taimake mu. Burina na ƙarshe shi ne; rubutuna ya karaɗe duniya ya kuma zama silar samun farin ciki ga duk wanda ya karanta yai amfani da shawara ko ƙwara ɗaya tal ne ya ɗauka, Allah yasa hakan ya zama mini sadaqatul jariyya ko bayan Raina. Alhamdu lillah.

Wace shekara ki ka fara rubutu?
Na fara rubutu tun ina Makarantar Sakandire, a lokacin ina aji uku zuwa huɗu 1982/ 83 kenan, na rinƙa rubuta gajerun labarai da wasan kwaikwayo wanda na kan ba malamanmu na Hausa su duba su yi min gyara, amma ban taɓa buga su ba, a lokacin ina rubutun ne kawai saboda sha’awa ko kuma idan mahaifina ya bani ‘assignment’, misali ya kan sayo min littafan Hausa na marubutan wancan zamanin, irin su, Magana Jari ce, Jatau na Ƙyallu, Wasan Marafa da sauransu, a gefe kuma ga jaridu irin su Gaskiya Tafi Kwabo, Amana da na Turanci duk zai haɗo min waɗanda idan na karanta ya kan nemi in faɗa masa darussan da na koya cikinsu, to maimakon in zauna in yi masa bayani baki da baki sai in samu littafi in rubuta.

Bayan mahaifina, mahaifiyata ta taka rawa wajen cusa min sha’awar rubutu ta hanyar tatsuniyya da take ba mu, kusan mun hardace kowacce tatsuniyar da ke cikin littafin marigayi Ibrahim Yaro Yahaya, ita ma ɗin da ta gama ba mu labarin za ta tambaye mu me muka koya, wane darasi muka ɗauka me kyau ko mara kyau. Ta haka sha’awar rubutun ya ginu sosai cikin zuciyata har ya zama min tamkar zazzaɓin da idan ya taso sai na riƙe alƙalami na amayar da abinda kwanyata ta tara na ke samun sukuni.

Bayan na yi aure ma na ci gaba da ‘yan rubuce-rubuce na da zaran na hango jigon da nike son gina labarina a kai, ina ajiye ‘Manuscripts’ ɗin, amma sai a shekarar 2000 Allah Ya ba ni ikon fara fitar da littafina na farko mai suna ‘Wani Jinkiri’ duk da ba shi na fara rubutawa ba. A jerin littafaina ‘Edge of Faith’ na fara rubutawa tun kafin in yi aure, ma’ana ina aji uku a sakandire don a lokacin na fi sha’awar rubutun ‘Novels ɗin Turanci, duk da ba wani zurfi na yi da jin harshen ba.

Daga ƙarshe wace shawara za ki bawa marubuta yan’uwan ki.
Shawarata ga ‘yan’uwa marubuta shine; mu ƙara riƙe mutuncin kanmu, mu san ƙima da darajar baiwar da Allah ya ba mu na hikima ba ‘yar ƙarama ba ce, ba kuma ya ba mu don mun fi wasu ba ne, aah, jarabawa ce a garemu wanda idan munyi taka tsan-tsan mun kiyaye abubuwan da muke rubutawa tare da tsabtace su, za mu samu sakamakon alkhairi gobe ƙiyama, mu cire ƙyashi da hassadar juna, mu rinƙa baiwa juna shawarwarin da su ka dace musamman matasan marubutan da su ka nemi taimakon daga manyan marubutan.

Zai yi matuƙar tasiri ƙwarai idan marubuta sun juya akalar rubuce-rubucensu ga muhimman abubuwan da ke neman gyara cikin ƙasarmu musamman a nan Arewa, misali kamar matsalar ta’addanci nan, sace-sacen mutane, almajiranci, fannin kiwon lafiya, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da cin zarafin ‘ya’ya mata har da yara mazan ma da sauran matsalolin rayuwa gasu nan birjik sun kutso kai suna addabar mu, ba mu tsaya da rubutu a kan jigon soyayya kaɗai ba, a kiyaye fassara ‘Novels, ko fim ɗin Indiyawa ko na ‘Koreans’, saboda wani labarin mutum na fara karantawa zai gano fim kaza ne aka fassara.

Sai kuma ina fatan Marubuta su yi ƙoƙarin haɗa kansu su zama tsintsiya maɗaurinsu ɗaya tare da addu’ar Ubangiji Ya ƙara mana hikima da basira, ya ci gaba da mana jagoranci kar ya bar mu da dabarar kanmu wajen rubuce-rubucen da muke yi, ya kuma ba mu ladan faɗakarwar da muke yi ta hanyar hikimar da Ya yassare mana, ya shafe dukkan kura-kurenmu na baya, da na yanzun da waɗanda za mu yi a gaba, ko da rayuwarmu ko bayan mun tafi.

Amin ya Allah Hajiya. Allah ya ƙara miki lafiya. Mun gode da lokacin ki.
Amin. Ni ma na gode.