Ciyaman Nda-Isaiah: Ba rabo da gwani ba…

Daga IBRAHIM SHEME

Tun a ranar farko da na fara haduwa da Mista Sam Nda-Isaiah, cikin mintuna kadan, ya dauke ni aiki. A lokacin ya na fafutikar neman wani qwararre wanda zai nada editan sabuwar jaridar sa mai suna LEADERSHIP, har wani tsohon dan jarida ya ba shi suna na. Rannan ya je Sakkwato domin nuna wa Gwamna Attahiru Bafarawa jaridar tasa, sai su ka hadu da wani aboki na a ofishin da su ke jira a yi wa kowannen su iso, domin ba tafiyar su daya ba, ba su ma san juna ba. Su na labari, sai abokin nawa ya fada masa cewar ai kuwa ya san ni. Kwanaki kadan bayan wannan haduwar tasu ne ni da aboki na mu ka tafi Abuja daga Kaduna domin mu gana da mawallafin a ofishin sa. Da ma ya na sauraren zuwan mu domin sun aje tun a Sakkwato cewa za mu je. Cikin minti kadan bayan ya nada ni edita, sai Mista Nda-Isaiah ya sanya ni aiki na farko duk da yake mun yi da shi zan fara aiki ne bayan mako daya: wato ya ce in rubuta filin ra’ayin edita na jaridar da za ta fito. Bayan na yi hakan, mu ka bar ofishin ina dauke da takardar nadi na a cikin aljihu na. Wannan ya nuna cewa shi mutum ne sha-yanzu-magani-yanzu a harkar kasuwancin sa.

Tun daga wannan lokaci na ci gaba da zama editan LEADERSHIP, wadda aka fara bugawa a ranar 24 ga Satumba, 2004, kuma na yi dadewar da babu wanda ya yi kamar ta a wannan muqamin. Mun fara ta a matsayin jaridar mako-mako, amma bayan shekara biyu sai na aje aikin, na tafi mu ka fara wani abu ni da wasu wanda bai dore ba. Shekara daya bayan bari na jaridar sa, sai Ciyaman (kamar yadda kowa a LEADERSHIP ya ke kiran sa) ya sake dawo da ni kamfanin. Da zan dawo, mu ka zauna a gidan sa da ke Kaduna don tattaunawa, ya ce in zabi dukkan sunan da na ke so a kira ni da shi, amma fa ban da “Ciyaman” ko “Babban Edita”, domin wadannan muqaman nasa ne. Sai na zabi muqamin “Shugaban Kwamitin Editoci”. Ni ne wanda ya fara riqe wannan muqamin a tarihin kamfanin.

Bayan kamar wata daya sai Ciyaman ya yi wani canji, ya nada ni editan jaridar wadda a lokacin ta kai shekara daya a matsayin mai fitowa kullum-kullum. Na riqe wannan muqamin na tsawon shekaru, har ta kai na gaji na ce masa ya nada wani ko kuma in aje aiki a kamfanin in yi tafiya ta. Daga nan Ciyaman ya nada ni Daraktan Editoci, mai kula da dukkan editocin jaridun da ya kakkafa. Qarshe dai na aje aiki a kamfanin ne a cikin 2010 lokacin da wata dama ta bude mani a wani wajen.

A cikin tsawon shekarun da na yi tare da Ciyaman, mun yi zama na dadi da rashin dadi duk a hade, kuma hakan ya danganta kan rana, lokaci da kuma al’amari. To amma a gaskiya zaman dadin ne ya fi yawa domin kuwa, duk da dan sabanin da mu kan samu jefi-jefi, zan iya cewa Ciyaman mutumin kirki ne.

Zan iya qirga lokutan samu da cigaba fiye da lokutan rashi ko bacin rai da na yi a tsawon shekarun da na yi a kamfanin. Na farko dai na samu qarin sanin makamar aiki da wayewa da abokai manya da qanana, da fice, da dai sauran su. Domin kuwa duk da yake Ciyaman mutum ne mai wuyar sha’ani a matsayin sa na shugaba, mai bayyanar da fushi a wasu lokutan, amma kuma mutum ne mai kirki. Na san ma’aikatan sa da yawa sun fi kallon irin matsin da ya ke yi, amma ni na fi tuno lokutan da ya ke kyautatawa, misali kamar wajen bada kyautar kudi ko littattafai da kuma uwa-uba shawara tagari. Kuma na fi kowa dadewa a matsayin edita ne saboda, ban da girmamawar da ke tsakanin mu ni da shi, na riga na gama naqaltar halayen sa, musamman abin da ke sa shi fushi da ma’aikaci. Yawancin mutane ba su san cewa na taba zama da wani ogan mai irin wannan halayyar ba, wato Alhaji Hassan Sani Kontagora (Magajin Rafi), wanda na taba zama Editan mujallar sa ta Rana da kuma ta Hotline.

Shekaru da dama bayan na bar LEADERSHIP (lura: dokar Ciyaman ita ce a riqa rubuta sunan jaridar sa da babban baqi!), na fahimci cewa dalilin da ya sa Mista Nda-Isaiah ya ke da matsi a kan ma’aikan sa ba wai don ya wulaqanta su ba ne, a’a, sai domin ya tabbatar da cewa sun cimma babbar nasara da nagartar aiki. Kamar mutum ne mai gina dalar gyada ko hanyar jirgin qasa wanda ya ke ganin idan bai matsa wa leburorin sa ba to ba zai iya cimma nasara a cikin lokacin da ya diba ba.

Dabarar sa ta yi aiki, domin kuwa ya fara wannan jarida ne a wani qaramin shagon buga komfuta, (wato business centre) a Kaduna lokacin da ya kafa wata qasidar labarai ta wata-wata mai suna LEADERSHIP CONFIDENTIAL, amma sai ga shi ya gina katafaren gidan jarida wanda kowa ya san shi a Nijeriya. A yau, kamfanin ya mallaki jaridu daban-daban da kuma hedikwata ta zamani, har da injinan buga jarida a tsakiyar birnin Abuja. A gani na, Ciyaman ya na kallon kan sa a matsayin daya daga cikin manyan mamallakan gidajen jaridu irin su abokin sa, mawallafin jaridar ThisDay, wato Mista Nduka Obaigbena, ko ma Baturen nan mamallakin jaridu da gidajen talbijin da na rediyo dan qasar Ostireliya, Mista Rupert Murdoch, kuma ba ya so a ce ya na bayan su can nesa.

A fagen aikin jarida a Nijeriya, Ciyaman babban mayaqi ne wanda ba ya gajiya, wanda a kullum ya ke kwatanta kan sa da manyan mawallafa irin su Mista Obaigbena da Mista Sam Amuka mai jaridar Vanguard, don a lissafa da shi a cikin wadanda su ka fi kowa. A wannan fage, ya kasance mugun madambaci wanda ba ya wasa da abokin karawa. Na tuna ranar da na sanar da shi cewa kamfanin Media Trust, wadanda su ne abokan gasar mu na kurkusa a Arewa, za su kafa jaridar Hausa. Ina rufe baki sai ya yi wuf ya ce, “Ya za a yi mu riga su?” Duk da yake ba mu riga su farawa din ba, to amma ba a dade da kafa jaridar Aminiya ba shi ma ya fito da jaridar LEADERSHIP HAUSA. Bayan shekaru ma sai da ya riga su wajen kafa jaridar Hausa mai fitowa kullum-kullum ta farko a tarihi, wato LEADERSHIP A YAU. Irin wannan zazzafan burin nasa na son gina babban kamfanin watsa labarai ne ya sanya a cikin ’yan shekarun nan ya ke ta haqilon ganin ya kafa gidan rediyo da na talbijin, wanda har gwamnati ta ba shi lasisin su.

To amma masu iya magana sun ce mutum na nasa, Allah na nasa. Kowane mai rai ya na da iyakar rayuwa, don haka dai Sam Nda-Isaiah ya cimma sa’i a ranar Juma’a, 10 ga Disamba, 2020. Na so a ce na gama wannan rubutun ba tare da na ambaci cewa ya rasu ba, domin abin da ciwo. Wai Ciyaman ya mutu! Duk da yake na samu labarin mutuwar cikin mintuna kadan da faruwar ta daga mawallafi kuma shugaban kamfanin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris, kuma na shafe kwana daya ina musayar jimami kan wanan rasuwa da dangin Ciyaman da editocin sa da abokai na da tsofaffin abokan aiki, ban gama fahimtar lamarin ba har sai da na ga jaridar Ciyaman da kan ta ta buga cewa ya rasu. Ya bar duniya har abada.

Labarin ya girgiza ni matuqa. Ban taba kawo wa Ciyaman mutuwa ba, musamman a yanzu ko ma nan gaba. Wani edita a kamfanin LEADERSHIP, da mu ke zancen, ce mani ya yi, “Ai ko shi Ciyaman bai kawo wa kan sa mutuwa nan da shekara talatin ba!” A gaskiya, ban taba kawo mutuwar sa a rai na ba duk da yake na sani qwarai da gaske cewa mutuwa rigar kowa ce, duk rai da Allah ya halitta sai ya dandana ta wata rana. A Musulunci, an yi kira a gare mu da mu yi tsammanin mutuwa a kowane daqiqa, kuma an ce ga kowane dan’adam “au sittuna, au saba’una” ce. Kenan saura ma shekara biyu Ciyaman ya cika sittin din, tunda ya mutu ya na da shekara 58 kacal. Mutuwa kenan, ba a sa maki rana! Ta zo ta dauke Kakaki Nupe a daidai lokacin da duniya ta na kai masa. Lallai ba rabo da gwani ba, kafin a sam gwani daga ne!

Shin yaya na ke kallon mutuwar Ciyaman? Duk da yake mun san cewa babban rashi ne aka yi a fagen aikin jarida a nahiyar Afrika ba ma a Nijeriya kadai ba, ni a gani na bai yi mutuwar banza ba. Saboda me? Ciyaman bai mutu ba tare da ya cimma wata nasara a rayuwa ba. Mutuwa ba ta dauke shi kafin ya yi wa al’umma aikin alheri ba. Gudunmawar da ya bayar ta na da yawa. Ga sawun sa da muryar sa nan a rubuce-rubucen da ya yi da kamfanonin da ya kafa, wadanda za a dade ana ganin su tare da jin su. Rubuce-rubucen sa su ne babbar nasarar sa, sai kuma kamfanonin sa. Wadannan su ne sakamakon gwagwarmayar da ya yi a rayuwa.

Damuwa ta ita ce me zai biyo bayan tafiyar sa? Rubuce-rubucen sa dai ba za su bace ba, musamman idan an tattara su an adana su a inda ya dace. To amma kamfanonin sa ne abin damuwar, musamman jaridun sa. Wadannan su na buqatar kulawar gaske. Ya kamata iyalin sa da shugabannin kamfanonin sa su yi tsayin daka wajen ganin jaridun sa sun dore. Ba za mu manta da yadda manyan jaridu da mujallu irin nasa su ka shude ba bayan mutuwa ko rabuwa ko karyewar arzikin wadanda su ka kafa su. Ga su nan birjik a Arewa. Don haka, don Allah a yi duk yadda za a yi a tabbatar da cewa hakan ba ta faru ga LEADERSHIP ba. Ciyaman da kan sa ya so ya yi gyare-gyaren da za su dora jaridun kan turbar dorewa ko bayan ran sa, amma sai Allah Ya sa bai aiwatar ba har ya koma ga Mahaliccin sa; kila a lokacin ya na hangen akwai lokacin da zai kammala shawara kan abin da ya dace ya yi. To yanzu ne ya kamata a cika masa burin sa. Yin hakan zai kasance babbar karramawa a gare shi. Shi kan sa zai yi murna idan aka yi hakan. Mu ma ’yan kallo za mu yi murna idan an yi hakan.