CJN ya sammaci manyan alƙalan kotunan Kano kan ba da umarni masu karo da juna

Babban Alƙalin Ƙasa (CJN), Justice Olukayode Ariwoola, sammaci Babban Alƙalin Kotun Tarayya da takwaransa na Babban Kotun Jihar Kano, kan su zo don ya ji yadda aka yi suka bayar da umarni masu cin karo da juna game da dambarwar sarautar Kano wanda hakan ya haifar da rashin tabbas.

Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alƙali S. A. Amobeda, ta ba da umarnin fitar da Muhammadu Sanusi II daga Fadar Ƙofar Kudu, tare da buƙatar a mai da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, kan kujerar Sarkin Kano.

A hannu guda, ita ma Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Amina Adamu Aliyu, ta ba da umarnin a bai wa Muhammadu Sunusi da muƙarrabansa kariya daga kowace irin barazana.

Haka nan, umarni ya hamramta raba Sunusi da da wasu muhimman kayan saraki da suka haɗa da tagwayen masu, malafar Dabo, takalman ɗawisu da sauransu.

Umarnin da kotunan suka bayar sun haifar da ruɗani game da ko wane ne Sarki a Kano. Duba da kowane ɓangare akwai umarnin kotun da ta nuna a ba shi kariya a matsayin sarkin Kano.

Yayin da Babbar Kotun Jihar ta ɗage sauraron ƙarar ya zuwa ranar 13 ga Yuni, ita kuwa Babbar Kotun Tarayya, ranar 4 ga Yuni ta ayyana a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraton ƙarar.

Yanzu dai jama’a sun zuba idanu tare da jiran gani da jin yadda za ta kasance bayan alƙalan biyun sun amsa sammacin Alƙalin Alƙalai na Ƙasa.