CMG ya samar da kyamara mai saurin ɗaukar hotunan bidiyo domin gasar wasannin Olympics ta Beijing

Daga CRI HAUSA

Babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin na CMG ya ƙera wata kyamara mai ƙarkon gaske, bisa fasahar “Ultra HD 4K” domin amfani da ita wajen ɗaukar hotunan bidiyo masu nagarta. Kyamarar dai na iya zarta gudun ‘yan wasan dake tsere a dandamalin ƙanƙara, yayin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing dake gudana yanzu haka.

An kafa kyamarar a cikin zauren tseren ƙanƙara na babban filin wasan hunturu dake birnin Beijing, inda kyamarar da aka yi wa laƙabi da “Cheetah,” kan yi gudun mitoci 25 ko wace daƙiƙa, wato kwatankwacin gudun kilomita 90 ko wace sa’a.

Bisa ƙiyasi, ‘yan wasan tseren ƙanƙara kan yi gudun mitoci 18 ne a duk daƙiƙa, kimanin kilomita sama da 60 zuwa 70 a duk sa’a, wanda hakan ke buƙatar samar da na’ura da za ya iya bin su da saurin gaske, domin ɗaukar motsi da suke yi, kamar ƙarin sauri da raguwar sa, da wuce juna, da yadda suke sarrafa jikin su yayin da suke gudu.

Shugaban sashen samar da kayayyakin aiki na CMG Zhao Wei, ya jagoranci tawagar da ta gwada aiki da wannan kyamara, bayan shafe tsawon lokaci ana gudanar da bincike da tsara aikin ta. Tun da fari, an kafa kyamarar ne a wajen harabar dandalin da ake gudanar da tseren, kafin samun amincewar amfani da ita daga kamfanin dake jagorantar watsa shirye-shirye, na kwamitin wasan Olympic na ƙasa da ƙasa IOC.