CNN ya ƙi ambatar Tinubu a matsayin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa

Ya bayyana Obi a matsayin wanda ya kamata a ayyana

Daga AISHA ASAS

Tashar talabijin na CNN ya ƙi bayyana Bola Tinubu a tsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, sai dai ya bayyana hasashen cewa, ɗan takara a Jam’iyyar LP,  Peter Obi, ne zai lashe zaɓen, abinda kawai ake jira shine, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta sanar cewa, shine zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da hukumar zaɓe ta yi na tabbatar da ɗan takara a Jam’iyyar APC, Bola Ahmad  Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen na shekarar 2023.

A cewar CNN, rahotanni kan ƙidayar ƙuri’u da suka samu daga wakilansu da ke lungu da saƙon mazaɓun Nijeriya ya sha bamban da wanda hukumar zaɓe ta bayyana, a cewar su, Peter Obi ne ya samu kaso chas’in bisa ɗari na ƙuri’un da aka samu, wanda hakan ne zai sa a ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Daga ƙarshe, tashar ta CNN ta ce, duk wani yunƙuri da ta yi na ganawa  da hukumar INEC daga can Ƙasar Amurka, don samun cikakken bayani, abin ya ci tura.