Corona: Tsoffin shugabannin Amurka uku sun amince da ayi musu allurar rigakafi

Tsoffin shugabannin Amurka guda uku, da suka hada da Bill Clinton, Barack Obama da George Bush, sun amince da ayi musu allurar rigakafi ta cutar Corona.

Shugabannin su uku, sun amince da ayi musu wannan rigakafi ne, saboda su zaburar da yan kasar su yadda da sahihancin wannan sabon rigakafi. Sai dai sun bada sharadin cewa, lallai sai hukumar magunguna da abinci ta kasar, ta baiwa sabuwar allurar rigakafin satifiket na amince wa da ingancin ta.

Fredy Ford wanda shi ne, babban jami’i a ofishin tsohon shugaban kasa George Bush, ya bayyanawa manema labarai cewa, tuni shugaban Bush ya tuntubi Dakta Anthony Fauci, wanda shine daraktan hukumar kula da cututtuka masu yaduwa na kasar da kuma babbar jamiar kula da cutar Corona ta fadar shugaban kasa, Dakta Deborah Birx domin ya ga irin gudunmowar da zai bayar wurin wayar da kan mutane a game da sabuwar allurar.

“Yan makonni da suka wuce shugaba Bush ya nemi in sanar da Mista Fauci da Mista Birx, cewa yana da aniyar ya bada gudunmawa wajen wayar da kan mutane a kowanne mataki, matukar wannan rigakafi ya samu sahalewar su” in ji mai magana da yawun tsohon shugaban.

Shi ma mai magana da yawun shugaba Clinton ya bayyana cewa “Shugaba Clinton ya amince da ayi masa wannan rigakafi a gaban kowa, in har yin hakan zai taimaka wurin zaburar da mutane su amince da ayi musu rigakafin” in ji Angel Urena.

A wata tattaunawa da yayi da SiriusXM, wacce za a saka ranar Alhamis, ya ce “in har Dakta Fauci ya amince da wannan rigakafi, to ko shakka babu, zan amince da ingancin ta”

Shi ma shugaba Jimmy Carter na cikin jerin tsoffin shugabannin kasar da ya bayyana amincewar sa da ta mai dakin sa Rossylin a game da wannan rigakafi. Wannan amincewa ta fito ne daga bakin asusun tallafi ba Jimmy Carter Foundation. Sanarwar dai ta yi kira ga al’ummar kasar da su rungumi wannan rigakafi da hannu biyu, sai dai ba su iya shaidawa manema labarai ko shi ma Mista Carter zai amince da ayi masa wannan allura a gaban jama’a ba.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*