Courtois ya kafa tarihi a Qatar bayan nasarar Belgium kan Kanada

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mai tsaron ragar Real Madrid da Ƙasar Belgium, Thibaut Courtois, ya kafa tarihi a Gasar Kofin Duniya na 2022 da ake gudanarwa a Ƙasar Qatar.

Tawagar ƙwallon ƙafar Ƙasar Belgium ta yi aiki tuƙuru wajen kare martabarta, inda ta lallasa ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta Ƙasar Kanada da ci ɗaya mai ban haushi, ta kuma riƙe wasan a haka har aka tashi a wasan gasar kofin duniya da suka fafata a ranar Laraba.

Kanada ce ta mamaye akasarin wasan na rukunin F, sai dai ta yi ta ɓarar da damarmakin saka ƙwallaye a raga, musamman a lokacin da ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga, wanda Alphonso Davies ya buga, amma mai tsaron raga na Belgium, Thibaut Courtois, ya hana ta shiga.

Yayin wasan na shekaranjiya, Courtois ya kafa tarihin iya tare bugun fenariti a na cikin tsaka da wasa a gasar ta Kofin Duniya, wanda rabon da a yi irin haka tun shekarar 1966 lokacin da Ingila ta lashe gasar, wanda ke nuna cewa, a cikin shekarar nan ne kaɗai mai tsaron raga ya yi nasarar tare fenariti har 5 cikin 9 da aka buga masa.

Haka zalika, Courtois ne mai tsraon raga ɗaya tilo da ya halarci gasar Kofin Duniya har sau uku a jere, wato a shekarar 2014 da 2018 da kuma yanzu 2022.

Courtois ya kuma tare ƙwallon da Alistair Johnston ya kusan saka masa a raga, kuma bayan haka ne Belgium ta samu dama, inda Michy Batshuayi ya karɓi ƙwallo daga Toby Alderweireld, ya kuma antaya a ragar mai tsaron ragar Kanada, Milan Borjan. 

Jonathan David shi ma ya ɓarar da wata damar saka ƙwallo a ragar Belgium, kana Courtois ya ture ƙwallon da Cyle Larin ya kusan cin sa.