Cross River: Shirin sauya sheƙar Gwamna Ayade ya kaɗa hanjin PDP

Daga UMAR M. GOMBE

Domin gudun kada ta rasa ɗanta, Jam’iyyar PDP ta tura a rarrashi Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade,
bayan da ta gano cewa gwamnan na shirin sauya sheƙa zuwa APC.

Binciken Manhaja ya gano cewa matakin sauya sheƙar da Gwamna Ayade ya ɗauka ba ya rasa nasaba da rasa ƙarfin ikon jan akalar PDP a jihar ga ‘yan majalisar ƙasa daga jihar kamar yadda ya bayyana yayin wani taro da suka gudanar kwannan nan.

Haka nan, Manhaja ta tattaro cewa ɗaukacin shugabannin ƙananan hukumomin jihar su 18 da kansilo
196 ba su saɓa wa umarnin gwamnan saboda cikakkiyar biyayyar da suke yi masa, inda su ma suka yi barzanar mara wa gwaman baya muddin ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya.

Da alama dai wannan batu ya kaɗa uwar hanjin PDP, inda tuni kwamitin jam’iyyar na ƙasa (NWC) ya haɗa kan wasu ƙusoshin jam’iyyar a kan su je su rarrashi gwamnan don hana shi sauya sheƙa.

Waɗanda PDP ta tura Cross River ɗin su ne; Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato da Godwin Obaseki na jihar Edo da kwamitin sulhu na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki, domin shawo kan Gwamna Ayade kan ya sake tunanin game da shirin nasa.

Shugaban ƙaramar hukumar Calabar, Effiong Eke, ya shaida wa manema labarai cewa bayan ganawa da NWC, sun buƙaci a sake sabon taron majalisar jiha don tabbatar da dawowar tsarin jam’iyyar ga Gwamna Ayade.

Yana mai cewa, “Gwamnan shi ne shugaban jam’iyyar a jihar. Ya kamata a ba shi ikon jan ragamar jam’iyyar, kuma ana iya yin hakan ne kawai ta hanyar shirya sabon taro.”

Tare da cewa muddin ba a sake haɗa wani taron ba, yana bada tabbacin duk inda Gwana Ben Ayade ya sa kai, su ma can suka yi.