Cutar koron: Zimbabwe ta karɓi tallafin allurar rigakafi daga Chaina

Daga FATUHU MUSTAPHA

Rahotanni daga ƙasar Zimbabwe sun nuna jirgin saman da ke ɗauke da allurar rigakafin annobar cutar korona wadda ƙasar Sin ta bayar gudunmawa ga ƙasar ya isa filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Robert Mugabe da ke Harare, babban birnin kasar, da asubahin wannan Litinin.

Da yake jawabi a filin jirgin, Mataimakin Shugaban Ƙasar Zimbabwe Constantino Chiwenga, ya ce ƙasar Sin ta jima tana taimaka wa Zimbabwe kan sha’anin yaƙi da annobar korona, kuma gudunmawar rigakafin zai taimaka wa ƙasar a yaƙin da take yi da annobar.

Kazalika, Chiwenga ya ce gudunmawar za ta yi tasiri wajen bai wa ƙasar damar farfaɗo da harkokin tattalin arzikinta da rayuwar yau da kullum.

A nasa ɓangaren, jakadan ƙasar Sin a Zimbabwe, Guo Shaochun, ya ce Sin ita ce ƙasa ta farko a duniya da ta mayar da hankali wajen samar da rigakafin korona don taimaka wa al ‘ummar duniya.

Yana mai cewa Zimbabwe na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da suka samu gudunmawar allurar rigakafin korona daga ƙasar Sin bisa mataki na farko, wanda hakan yana ƙara nuna irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *