Cutar Korona: Ƙarin mutum 49 sun harbu a Nijeriya

Daga UMAR M. GOMBE

Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta ce a halin yanzu adadin mutane da suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasa ya kai 166,816 bayan da aka samu ƙarin mutum 49 da suka harbu da cutar a tsakanin sa’o’i 24 da suka gabata.

NCDC ta ba da wannan bayani ne a shafinta na intanet. Inda ta ce ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi ne da suka haɗa da Ondo mai mutum 30, Legas na da 15, Kaduna na da 2, sannan Gombe da Adamawa kowacce na da ɗai-ɗai.

A cewar NCDC, tun bayan ɓullar cutar a Nijeriya ranar 27 ga Fabrairun 2020, mutane 2,117 ne cutar ta yi ajalinsu, yayin da mutum 163,190 sun warke bayan da aka yi musu magani.

Cibiyar ta ƙara da cewa, yanzu haka mutum 1,509 suke ɗauke da cutar wanda kuma ana ci gaba da ba su kulawar da ta dace.

Haka nan, ta ce tun bayan ɓullar cutar ta yi gwaje-gwajen da suka kai 2,180,444.

A hannu guda, Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), ta ce ‘yan Nijeriya 1,966,548 ne suka yi allurar rigakafin koron kashin farko, sannan ya zuwa Litinin da ta gabata mutum 358,239 sun samu yin rigakafin kashi na biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *