Cutar Korona: An samu ƙarin mutum 1,340 da suka harbu a faɗin ƙasa

Daga FATUHU MUSTAPHA

A halin da ake ciki, birnin tarayya, Abuja da jihar Legas da River da kuma Oyo, su ne jihohin da ke kan gaba wajen samun mafi yawan waɗanda suka harbu da cutar korona a tsakanin sa’o’i 24 da suka gabata.

Bayanan Cibiyar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), sun nuna an samu ƙarin mutum 1,340 da suka kamu da cutar korona. Ƙarin da cibiyar ta ce ya shafi wasu jihohin ƙasar nan su 22, ciki har da Abuja 320, Lagos 275, Rivers 117, da kuma Oyo 100.

Sauran sun haɗa da Sakkwato 3, Kaduna 31, Katsina 14, Ebonyi 48, Kano 24, Edo da Osun kowacce na da 29, Adamawa 42 da dai sauransu.

NCDC ta ce, kawo yanzu adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da korona a faɗin ƙasa ya kai 136,030.
Sannan mutum 110,449 sun warke, an kuma sallame su. Kana mutum1,632 sun mutu sakamakon annobar.