Cutar korona: An yi wa ƙusoshin gwamnati rigakafi

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Yaƙi da Cutar Korona (PTF), Boss Mustapha, tare da sauran mambobin kwamitin na PTF sun karɓi allurar rigakafin cutar korona.

An yi musu allurar ne a lokacin da PTF ke gabatar da bayanan ayyukansa kanar yadda ya saba a Abuja.

Mustapha wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, shi ya soma karɓar allurar wanda aka yaɗa kai tsaye a talabijin kafin daga bisani sauran jami’an suka karɓi tasu.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, shi ma na daga cikin waɗanda suka karɓi allurar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *