Cutar Korona: Babu buƙatar sake kulle Kano – Ganduje

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta kafa dokar kulle ba don yaƙi da cutar korona.

Ganduje ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da jami’ai na musamman su 2000 kan yaƙi da cutar korona a jihar wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar a Lahadin da ta gabata.

Idan dai za a iya tunawa, ko a bara gwamnatin Kano ta kafa dokar kulle a jihar a matsayin wani mataki na daƙile yaɗuwar korona.

Da yake magana yayin ƙaddamarwar, Gwamna Ganduje ya ce, “Gwamnati ba ta ga dacewar sake sanya dokar kulle a jihar ba kamar yadda ta yi a shekarar da ta gabata duba da irin tasirin da dokar ta yi ga tattalin arzikin jama’arta.

“Amma muna ƙoƙarin ganin mun kare al’umarmu daga barin kamuwa da annobar.”

A cewarsa, “Kwamitin da muka kafa kan yaƙi da annobar na matuƙar ƙoƙarin aiwatar da aikinsa. Kum zai ci gaba da tabbatar da cewa ‘yan jihar na martaba dokokin da aka shimfiɗa don daƙile yaɗuwar cutar.”

Jami’ai na musamman da gwamnan ya ƙaddamar sun ƙunshi jami’an tsaro da malamai da sarakuna da ‘yan jarida da jami’an kiwon lafiya da dai sauransu, waɗanda aka ɗora wa aikin wayar da kan al’umma da tabbatar da bin dokokin yaƙi da cutar korona.