Daga WAKILINMU
Rahotanni daga Ƙasar Saudiyya, sun nuna a tsakanin sa’o’i 48 da suka gabata, mutum ɗaya kacal aka samu ya harbu da cutar korona a birnin Madina.
Bayanai sun nuna wannan wata alama ce da ke nuni da yiwuwar samun zarafin aiwatar da Hajjin bana.
A halin yanzu dai maniyyata daga sassan duniya, na ci gaba da fatan samun nasarar karya lagon annobar korona domin bada damar yin Hajjin 2021 cikin salama.