Cutar korona ta yi ajalin matar tsohon Shugaban Ƙasa, Sehu Shagari

Allah Ya yi wa matar tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari, Hajiya Hadiza Shagari rasuwa.

Sanarwar da ta fito daga ahalin marigayiyar ta hannun Capt. Muhammad Bala Shagari (rtd), ta nuna Hajiya Hadiza ta rasu ne a safiyar Alhamis samakon cutar korona.

A cewar sanarwar, “Cikin alhini muna sanar da rasuwar mahaifiyarmu, Hajiya Hadiza Shehu Shagari, matar tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR (Turakin Sokoto).

“Mun rasa ta ne da safiyar Alhamis, 12 ga Agusta, 2021 da misalin ƙarfe 3 na asuba bayan ta yi fama da cutar korona a cibiyar killace mutane da ke Gwagwalada, Abuja.”

An yi jana’izar marigayiyar a Abuja da misalin ƙarfe huɗu na yamma a wannan Alhamis daidai da karantarwa addinin Musulunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *