Cutar korona: Yau Nijeriya za ta karɓi rigakafin Johnson & Johnson guda 176,000

A wannan Laraba ake sa ran Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin korona samfurin Johnson & Johnson har guda 176,000, in ji shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Dr. Faisal Shuaib.

Wannan na zuwa ne kimanin mako ɗaya da karɓar rigakafin korona samfurin ‘Moderna’ kimanin milyan 4 daga gwamnatin Amurka.

Shuaib ya ce abin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta yi jinkiri wajen yi wa ‘yan ƙasa rigakafin ‘Moderna vaccine’, shi ne don gudanar da bincike da kuma bai wa hukumarsu damar yin aiki tare da Hukumar Kula da Ingangancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) wajen samun nasarar rarraba maganin zuwa cibiyoyin da suka dace.

Yayin wani taron mana labarai a Anuja, Shuaib ya ba da tabbacin cewa, a yau Laraba Nijeriya za ta karɓi rigakafin cutar korona samfurin Johnson & Johnson guda 176,000.

Ya ce kamar yadda aka sani, rigakafi 176,000 da Nijeriya za karɓa ɗin ɓangare ne na rigakafin korona guda 29,850,000 da Gwamnatin Tarayya ta sayo daga Bankin AFREXIM ta hannun Ƙungiyar Haɗa Kan Ƙasashen Afrika (AU).