Cutar mashaƙo ta kashe yara da dama a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Wasu majiyoyi a Potiskum ta jihar Yobe sun bayyana cewa ana kyautata zaton ɓullar sabuwar cutar mashaƙo a garin inda a halin yanzu an samu mutuwar yara da dama yayin da aka kwantar da wasu a cibiyoyin killace majinyata a sibitin garin.

Dr. Umar Chiroma, shi ne muƙaddashin babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Yobe, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Lokacin da muka samu rahoton ɓullar cutar a garin Potiskum a ƙarshen mako, nan take muka haɗa tawaga zuwa wuraren da abin ya shafa don wayar da kan jama’a tare da daƙile yaɗuwar ta cikin al’umma. Duk da a yanzu, ba za mu iya bayyana shi a matsayin Diphtheria ba har sai mun ɗauki samfurin ƙwayar cutar mu yi bincika daga nan za mu iya sanar da abin da yake ciki.”

‘’Har wala yau kuma, wasu daga cikin majinyatan sun haura shekaru 30 wasu 14 yayin da wasu kuma ‘yan shekara 12 zuwa 8 ne. Sannan wani abin takaici shi ne, wasu daga cikin majinyata suna daga cikin wadanda suka bijirewa allurar riga-kafi, wanda hakan ya sa ya fi shafar yaran da ba su yi riga-kafin ba.” In ji shi.

Dr. Chiroma ya ƙara da cewa, ‘’Wasu daga cikin majinyatan sun warke, don haka ba za mu iya tabbatar da cewa cutar Diphtheria ce har sai idan binciken masana ya gano ita ce. Amma da safiyar yau na samu labarin ɓullar cutar daga daraktan da yake kula da wannan shiyya, saboda haka har yanzu ba mu sami adadin mace-macen a hukumance ba.”

Bayanan sun ƙara da cewa, unguwanin da abin yafi kamari sune unguwar Tandari, Misau Road, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Kasa, Boriya, Yuganda da Texaco Quarters su ne yankunan da lamarin ya fi shafa.

Wata majiya daga cibiyar keɓance majinyata na asibitin ƙwararru da ke Potiskum ta bayyana cewa suna fuskantar ƙarancin magungunan da za su shawo kan lamarin.

Wata majiya ta shaidawa wakilinmu cewa sama da mutum 46 ne aka kwantar a asibitin, inda yara 20 ne suka mutu a gida tare da ƙarin wasu 4 da suka mutu a asibitin.

Abdullahi Muhammad, daga garin na Potiskum ya ce ‘’Yara da dama sun mutu a gida kafin a kai su asibiti, wannan cuta ce mai saurin kisa.”

‘’Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakin ceto rayukan jama’a, daga wannan cuta wadda mun lura ta na ɗauke da zazzabi, tari, kashe jiki da sauransu.”

A nashi ɓangaren, jami’in kula da riga-kafi na Ƙaramar Hukumar Potiskum, Malam Buba, ya musanta alƙaluman waɗanda suka mutu ta sanadin cutar, amma ya ce a ƙalla yara 42 ne ke kwance a asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *