*Ya zama Shugaban Ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Afirka
Daga BASHIR ISAH
An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa don ci gaba da jan ragamar mulkin ƙasar.
Da wannan Faye mai shekara 44, ya zama shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a nahiyar Afirka.
Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe babban zaɓen ƙasar, Faye ya sha alwashin yin sauye-sauye da dama a ɓangarori daban-daban na ƙasar.
An rantsar da Faye ne a ranar Talata a birnin Diamniadio da ke kusa da Dakar babban birnin ƙasar.