Da ɗumi-ɗumi: ƴan Bindiga sun sace mahaifiyar ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya A.A Zaura

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun yi garkuwa da mahaifiyar ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura, wanda aka fi sani da A.A Zaura.

Rahotanni sun nuna cewa da sanyin safiyar Litinin din nan ne aka sace mahaifiyar ɗan siyasar, Hajiya Laure Mai Kunu kafin kiran Sallar Asubahi.

Shugaban ƙaramar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase, ya ce jami’an tsaro sun sanar da shi lamarin a hukumance.

Ya ce an yi garkuwa da Hajiya Laure ne a gidanta da ke unguwar Rangaza a ƙauyen Zaura na karamar hukumar.

Haka kuma, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Kiyawa ya shaida wa Solacebase cewa, an tura tawagar ƴan sanda na Puff Adder yankin domin kuɓutar da ita tare da kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *