Hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC), ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, a gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama.
Ana sa ran Bello zai amsa tuhume-tuhume 16 da suka shafi zargin almundahanar Naira biliyan 110.
A tuna cewa tsohon gwamnan ya miƙa kansa ga EFCC a ranar Talata bayan dogon wasan ɓuya da ya yi da hukumar.
Sanye da farar riga da kuma hula mai shuɗi, jami’an tsaro na EFCC suka raka shi zuwa harabar kotun don gurfanarwar.