Da Ɗumi-Ɗumi: An rantsar da Okpebholo na APC a matsayin sabon gwamnan Edo

Daga BELLO A. BABAJI

An rantsar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Edo a wani yanayi na kafa tarihi, a Benin babban birnin jihar.

An gudanar da taron rantsarwar ne a ranar Talata, a filin wasa na Samuel Ogbemudia dake cikin birnin.

Hakan na zuwa ne watanni biyu bayan jam’iyyar APC ta lashe zaɓen gwamna a jihar.

Okpebholo ya kama karagar mulki ne inda zai kasance tare da abokin tafiyarsa, wato Dennis Idahosa.

Gwamna mai barin gado, Godwin Obaseki ya jagoranci jihar har sau biyu inda wa’adinsa na ƙarshe ya kare a yau, 12 ga watan Nuwamba, 2024.