Da ɗumi-ɗumi: APC ta ɗage shirin tantance ‘yan takarar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC ta ɗage shirin tantance ‘yan takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙarshin jam’iyyar zuwa 23 ga Mayu.

APC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan janye ra’ayin shiga takara da wasu ‘yan takarar suka yi.

A cewar jam’iyyar, za ta tantance ragowar ‘yan takarar nata ya zuwa sabuwar ranar da ta tsayar.