Daga BASHIR ISAH
Kwamitin Shugabanni na Ƙasa (NEC) na Jam’iyyar APC, ta zaɓi tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Kazalika, jam’iyyar ta zaɓi tsohon mai magana davyawun Shugaban Majalisar Dattawa, Ajibola Basiru, a matsayin sakatarenta na ƙasa.
Kwamitin (NEC) ya yi wannan zaɓen ne yayin zamansa karo na 12 da ya gudanar ranar Alhamis Transcorp Hilton da ke Abuja.
Mahalarta taron sun haɗa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, gwamnonin APC da sauransu.
Sai dai, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo na daga cikin mambobin APC waɗanda ba a ga fuskokinsu a wajen taron ba.
Da yake yi wa taron jawabi, Shugaba Tinubu ya ce bayan lashe zaɓe da APC ta yi, yanzu lokaci ne da za a cika wa ‘yan Nijeriya alƙauran da aka yi musu.
Tinubu ya jaddada cewa zaɓen 2023 shi ne zaɓe mafi inganci da aka samu a Nijeriya.