
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da haɗa ƙungiyar haɗakar jam’iyyun adawa don neman galaba akan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Abuja, ranar Alhamis.
Sauran jagororin da suka halarci taron sun haɗa da ɗan takarar Shugaban ƙasa a jami’yyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, wanda Yunusa Tanko ya wakilce shi; tsohon Sakataren Gwamantin Tarayya, Babachir Lawal; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; Sakataren ƙungiyar haɗakar jam’iyyun siyasa, Peter Ahmeh da Segun Showunmi da sauran su.
Sun kuma yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Jihar Ribas da dakatar da gwmanan jihar da mataimakiyarsa da ƴan Majalisar Dokoki a jihar da ya yi.