
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani tsohon Alƙali a Kano mai suna Muntari Ɗandago, ya musanta kalaman wata sananniyar mai harkar kayan mata kuma tsohuwar tauraruwa, Sadiya Haruna inda ta ce ya kan ziyarci gidanta akai-akai domin cin abinci da kuma kwana.
Ya ce, kalaman nata yunƙuri ne na masa sharri da kuma ɓata masa suna bayan ko shi mutumin kirki ne a idon jama’a.
A watan Fabrairun 2022 ne Ɗandago a matsayinsa na Alƙali a wata Shari’a da ya jagoranta, ya yanke wa Sadiya hukunci zaman gidan yari na wata shida kan samun ta da laifin ɓata wa tsohon mijinta, Isa Isa suna.
Sai dai, a lokacin da a ke hira da ita a shirin ‘Gabon’s Talk show’s, Sadiya ta ce Ɗandago “ya yaudare ta na tura ta gida kaso da ya yi duk da kasancewarsu abokai”, inji ta.
A wata hira da jaridar ‘DAILY NIGERIAN’, Ɗandago ya ce maganarta a kansa ƙarya ce, sannan irin haka na daga cikin ƙalubalen da jajirtattun ma’aikata irin sa ke fuskanta kan ayyukansu.
Tsohon Alƙalin ya ƙara da cewa, wannan ba shi ne karo na farko da ta yi makamancin kalaman ba, domin ko lokacin da ake tsaka da shari’ar ta faɗi wanda ya fi wannan, saboda haka za a iya zuwa a yi bincike.
Sadiya ta kuma bayyana wa al’umma cewa, ta karɓi hukuncin ne matsayin ƙaddara ga rayuwar ta sannan ta kuma yi tsokaci kan abinda ya lalata aurenta da shahararren ɗan ‘TikTok’, Al’amin G-Fresh inda ta ce ya saɓa alƙawuran da suka yi kafin su yi aure.
Cikin abin da ya raba auren nata da ɗan TikTok ɗin akwai batun gwajin cutar HIV da biyan rabin kuɗin hayar gida (500,000) da ƙaurace wa aikata masha’a kafin aure, sannan akwai kuma batun kasancewarsa mara ƙarfin saduwa, kamar yadda jaridar Alfijir ta ruwaito.