Da Ɗumi-ɗumi: Emefiele ba ya hannunmu – DSS

Daga BASHIR ISAH

Hukumar tsaro ta DSS ta musanta cewa tana tsare da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, kamar yadda aka yaɗa da farko.

Da fari rahotannin da aka yaɗa a kafafe mabambanta sun nuna hukumar tsaro (DSS) ta cika hannu da Emefiele jim kaɗan bayan aka sanar da dakatar da shi daga matsayinsa a ranar Juma’a.

Sai dai da yake mayar da martani ga rahoton, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya bayyana a ranar Asabar cewar, “A yanzu dai Emefiele ba ya hannun DSS.”

A ranar Juma’a Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya sanar da batun dakatar da Emefiele da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Inda ya ce, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugaban Bankin Nijeriya, Mr Godwin Emefiele, CFR, nan take.”