Da Ɗumi-Ɗumi: Fubara ya janye ƙalubalantar Kakaki Amaewhule kan Majalisar Dokokin Ribas a Kotun Ƙoli

Daga BELLO A. BABAJI

Kotun Ƙoli a Abuja, ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya yi game da ƙalubalantar shuagabancin Majalisar Dokokin jihar.

Ta kuma umarci Fubara da ya biya tarar Naira miliyan biyu ga majalisar da Amaewhule ga kwamitin mutane biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji a ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne a lokacin da lauyan gwamnan, Yusuf Ali, ya janye ƙarar.

Sauran bayanai za su zo daga baya…