
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Nassarawa, Abdullahi Sule ya miƙa sunayen mutane 16 ga Majalisar Dokoki don tantance su a matsayin waɗanda za su zama sabbin kwamishinonin ma’aikatu a jihar.
Guda shida daga cikin su suna daga cikin sahun waɗanda aka rushe a kwanakin baya, yayin da biyu kuma mambobi ne na majalisar.
Kakakin Majalisar Rt. Hon. Ɗanladi Jatau, ya bayyana hakan a yayin zaman majalisar a Lafiya, ranar Litinin.
Ya yi kira ga waɗanda aka bada sunayen nasu da su miƙa kwafin takardun su (CV), guda 30 ga majalisar daga yanzu zuwa ranar Alhamis na wannan makon, yayin da a ranar Litinin kuma sai su halarci zaurenta domin tantance su.
Waɗanda gwamnan ya aika da sunayen nasu sun haɗa da Yakubu Kwanta daga ƙaramar hukumar Akwanga, Hon. Tanko Tunga daga Awe, Hajiya Munirat Abdullahi da Gabriel Agbashi daga Doma, Barista Isaac Danladi Amadu daga Karu, Princess Margret Otaki Elayo daga Keana, Dr. Ibrahim Tanko daga Keffi da kuma Dakta John DW Mamman daga Kokona.
Sauran sun haɗa da Hon. Aminu Mu’azu Maifata da CP Usman Baba (Mai Ritaya) daga Lafia, Hon. Mohammed Sani Ottos daga Nasarawa, Hon. Mohammed Agah Muluku daga Nassarawa Eggon, Barr. David Moyi daga Obi, Dr. Gaza Gwamna daga Toto da Barista Judbo Hauwa Samuel da kuma Hon. Muazu Gosho daga ƙaramar hukumar Wamba.