Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnan Nasarawa ya naɗa sabon sakataren gwamnati da sallamar wasu muƙarrabansa

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya naɗa tsohon Antoni-Janar na jihar, Labaran Shuibu Magaji a matsayin Sabon Sakataren Gwamnatinsa (SSG).

A yayin bikin naɗin sabon SSGn ne, gwamnan ya yi kira a gare shi da ya tabbatar da gaskiya da adalci a gudanar da lamuran gwamnati tare da amfani da ƙwarewarsa don amfanar da jihar da al’ummarta.

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na amfani da kadarorin gwamnati wajen aiwatar da tsare-tsare da shirye-shirye don ci-gaban harkar tattali a jihar tare da yaƙar duk wata hanya ta rashawa.

AA Sule ya kuma kori baki ɗaya waɗanda ya bai wa muƙaman siyasa da suka haɗa da masu ba shi shawara na musamman, manyan masu taimaka masa na musamman da masu taimaka masa kan ayyuka da kuma mataimaka kan ayyuka na musamman.

Haka kuma, ya naɗa Komodo Yahaya Owuna Mai ritaya a matsayin jagoran yankin Udege don warware matsalolin rikicin ƙabilanci na ƙauyukan ƙabilar Afo da kuma taimaka wa gwamnati a ƙoƙarinta na samar da mafita ta dindindin.