Da Ɗumi-ɗumi: Ibrahim Gusau ya lashe zaɓen NFF

An zaɓi Alhaji Ibrahim Musa Gusau a matsayin sabon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF).

An zaɓi Gusau a wannan muƙamin ne yayin zaɓen NFF karo na 78 da ya gudana a Benin, babban birnin Jihar Edo a ranar Juma’a.

Sakamakon zaɓen ya nuna Gusau ya samu ƙuri’u 21 wanda hakan ya ba shi nasara a kan tsohon Mataimakin Shugaban hukumar na 1, Barista Seyi Akinwunmi wanda ya samu ƙuri’u who got 12 kacal.