Da ɗumi-ɗumi: Jirgin saman Nijeriya zai soma aiki a Afrilun 2022

Daga BASHIR ISAH

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Hadi Sirika, ya bayyana cewa ana sa ran jirgin saman Nigeria Air zai soma aiki ya zuwa Afrilun 2022.

Sirika ya bayyana haka ne sa’ilin da yake zantawa da wakilan jaridu a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zaratarwa a ranar Laraba.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, shi ne wanda ya jagoranci taron na ranar Laraba.

A cewar Sirika, zirga-zirgar jirgin a cikin ƙasa zai kasance ne a ƙarƙashin kulawar wani kamfani inda gwamnati ke da hannun jari na kashi 5% a ciki.

Ya ci gaba da cewa, ‘yan kasuwar Nijeriya na da kashi 46%, sannan kashi 49% da ya rage za a jiye shi ga ‘yan kasuwar da za su shigo a yi da su haɗa da masu zuba jari daga ƙetare.

Kazalika, ya ce idan jirgin ya soma aiki yadda ya kamata, ana sa ran hakan ya samar da gurbin aiki guda 70,000 ga ‘yan Nijeriya.