Da Ɗumi-ɗumi: Jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a Legas

Wani jirgin sama mai saukar ungulu da ba a kai ga tantancewa ba ya yi hatsari a yankin Oba Akran Ikeja a Jihar Legas.

An ce jirgin ya faɗa wani gini ne kana daga bisani ya kama da wuta a wannan Talatar.

Majiyarmu ta ce an samu ceto mutum huɗu da ke cikin jirgin da ransu in ji wani jami’in hukumar NEMA.

Ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga gano dalilin aukuwar hatsarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *