Da Ɗumi-ɗumi: Kano ta zama ta Abba Yusuf

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe INEC, ta tabbatar da ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Abba ya taki wannan matsayi ne bayan da ya samu ƙuri’u 1,019,602 wanda hakan ya ba shi damar doke babban abokin hamayyarsa na APC kuma Mataimakin Gwamnan jihar mai ci, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya tsira da ƙuri’u 890,705 a zaɓen.

INEC ta ce Muhammad Sani Abacha na Jam’iyyar PDP, shi ne ya zo na uku da ƙuri’u 15,957.

Da safiyar wannan Litinin INEC ta ayyana Abba sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Kano mai jiran gado.

Wani ala’amari mai ɗaukar hankali da Manhaja ta gano game da nasarar da Abba ya samu, shi ne yadda ƙananan yara da sauran mata a jihar suka mamaye tituna suna nuna murnarsu.

Rundunar ‘yan sanda jihar dai ta yi gargaɗin kada jama’a su fito kan tituna don zagayen murnar lashe zaɓe, lamarin da ta ce ba za ta saurara wa duk wanda ta kama da aikata hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *