Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da ba a ga lauyoyinsa ba, Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta ƙi amincewa da buƙatar hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.
An shirya sauron ƙarar ne da aka shigar a gaban Alƙali Emeka Nwite kan tuhumce-tuhumce guda 19 da aciki akwai zarginsa da badaƙalar Naira biliyan 80.2.
A lokacin da aka kira sauraron hukunci game da ƙarar tsohon gwamnan, babu ɗaya daga cikin lauyoyinsa da suke wajen inda daga nan ne wakilin ɓangaren EFCC, Mista Kemi Pinheiro ya nemi kotun ta bar hukumar ta gurfanar da Bello.
A lokacin da aka tambayi tsohon gwamnan kan dalilan da suka sanya ba a ga lauyoyin nasa ba, sai ya ce bai samu labarin zuwa kotun ba sai ƙarfe 11 na safiyar ranar Alhamis.
Sauran bayanai za su zo daga baya….