Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan Jihar Nasarawa, ta tsige Injiniya Abdullahi Sule a matsayin Gwamnan Jihar Nasarawa.
Biyu daga cikin alƙalan kotun su uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ezekiel Ajayi, sun bayyana ɗan takarar Jam’iyyar PDP, David Umbugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da ya gudana a wannan shekarar da ake ciki.
Ya zuwa haɗa wannan labarin alƙali na, Jastis Ibrahim Mashi, bai kai ga bayyana nasa hukuncin ba.