Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bada belin Emefiele

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ta bada belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Kotu ta bada belin yayin zaman da ta yi a ranar Laraba domin sauraren ƙarar neman beli da Emefiele ya shigar.

Mai Shari’a Olukayode Adeniyi ne ya bada belin tare da miƙa Emefiele ga lauyoyinsa inda ake sa ran su gabatar da shi a Babbar Kotun Abuja a ranar 15 ga Nuwamba kotun da a nan ne EFCC ta shigar da ƙara a kan Emefiele da wani.

Lauyoyin da kotun ta miƙa wa Emefiele su ne Matthew Burkaa (SAN) da Johnson Usman (SAN) da kuma Magaji Ibrahim (SAN).

EFCC ta gabatar da Emefiele ɗin ne don cika umarnin da Babbar Kotun Tarayyar ta ba ta kan ta saki Emefiele ba tare da wani sharaɗi ba ko kuma ta gabatar da shin a kotu don sauraren ƙarar neman beli da ya shigar

Emefiele ya shafe sama da kwana 149 tsare a hannun EFCC kafin ta gabatar da a kotu a wannan Laraba.