Daga BASHIR ISAH
Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPC) mai zamanta a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta bai wa Hukumar Zaɓe (INEC), umarnin ta bai wa zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado Bola Tinubu, damar bincikar muhimman kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanarda zaɓen Shugaban Ƙasa.
Tinubu da Jam’iyyar APC sun buƙaci kotu ta ba su damar duba kayayyakin zaɓen ne domin tattara bayanan da za su yi amfani da su wajen kare kansu a kotu daga ƙara da aka shigar a kansu.
‘Yan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi, sun shigar da ƙara kotu suna ƙalubalantar nasarar da Tinubu ya samu na lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gudana.
“Kayayyakin za su taimaka mana wajen kimtsawa don kare kanmu da kuma kwatanta bayananmu da na wajen INEC,” in ji lauyan Tinubu, Mr. Akintola Makinde.