Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta tabbatar da Yahaya a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Gombe

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Gombe ta tabbatar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Yayin zamanta a ranar Talata, kotun ta yi watsi da ƙarar da aka shigar inda ake ƙalubalantar nasarar lashe zaɓen da Yahaya ya yi.

‘Yan takaran jam’iyyun hamayya a jihar, wato Jibrin Barde na PDP da Nafiu Bala na ADC, su ne suka shigar da ƙarar inda suka nuna rashin gamsuwarsu da sake zaɓen Inuwa Yahaya da Mataimakinsa, Manassah Daniel Jatau da aka yi a matsayin shugabannin jihar ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Duka alƙalan kotun su uku, sun yi ittifaƙi kan watsi da ƙararrakin.

Kotun ta bayyana ƙarar da ɗan takarar PDP ya shigar a matsayin mara tushe, wanda hakan ya sa ta yi watsi da ita.

PDP ta yi ƙorafin cewa an tafka ƙazamin maguɗi yayin zaɓen.

Yayin da a hannu guda kotun ta ce ƙarar da ADC ta shigar ba ta da darajar da kotu za ta saurare ta, don haka aka kori ƙarar.